Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Allah Ya Yiwa Baba Goni Malam Karami Na Garin Potiskum Rasuwa.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji,un.

 

A Yau Laraba Allah Yayiwa Babban Gwanin Al-Qu’ranin Baba Goni Malam Karami Na garin Potiskum Rasuwa.

 

Insha ALLAHU, da yammacin yau laraba za’ayi jana’izar sa a nan tsangayar sa.

 

Tabbas Duniyar Makaranta Al-Qu’rani munyi Babban Rashi na babban Malami Mai darasu Kuma Uba Ga Manyan Gwanayen Al-Qu’rani.

 

Allah yayi masa Rahma yasa Mutuwa hutu ce in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani Albarakcin Annabi da Al-Qu’rani. Amiiiin Yaa ALLAH

 

Daga: Mu Koma Tsangaya 9/10/2024

Share

Back to top button