Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Allah Ya Yiwa Babban Malamin Sheikh Habib Abubukar Adnan Rasuwa.

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un 😭😭

 

Babban malamin Musulunci a duniya ya rasu a kasar Jordan Sheik Habib Abubukar Adnan.

 

Babban abin bakin-ciki nake sanar daku rasuwan babban malamin a wannan zamanin namu a fagen ilimin fiyayyen halitta da zamantakewa ta mahangar Musulunci (‘ilm ul-Ākhir al-Zamān), Habib Abubakar al-‘Adanī, ya rasu, dake jihar amman a kasar Jordan.

 

Allah ya jaddada masa rahma ya gafarta masa, Allah ya kara kusanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ﷺ.

 

Allah ya tashe shi tare damu da shugaban mu Sayyiduna Muhammad (SAW) a cikin mafi daukakar Aljannah. Amiin

 

Daga: Babangida A. Maina

Founder CEO Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button