Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un: Allah Ya Yiwa Daya Daga Cikin Malaman Musulunci Rasuwa.

Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un

 

أَلَا إِنَّ أَوْلِيَاءَ اللَّهِ لَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ 💧 الَّذِينَ آمَنُوا وَكَانُوا يَتَّقُونَ💧لَهُمُ الْبُشْرَىٰ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الْآخِرَةِ ۚ لَا تَبْدِيلَ لِكَلِمَاتِ اللَّهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ💧

 

Mun yi rashin Jagora a Musulunci a garin Jos, babban limamin Masallaci wato SHEIKH MUHAMMAD LAWAL ADAM, JOS.

 

Babban Shehi ne na tarbiyyar ruhi cikin Darikar Tijaniyya, da kuma Faidar Sheikh Ibrahim Nyass, Radiyallu Anhum wa Ardahum wa Anna Bihim.

 

Ɗaya ne cikin manyan Almajiran Shehu Malam Tijjani Zangon Bare-bari, kuma hadimin sa na gaske. Duk wanda ya taɓa karo da wani abu na rubutu daga Sheikh Malam Tijjani bn Usman, kuma yaga an saka ‘بقلم محمد آدم جوس’ ma’ana da alƙalamin Muhammad Lawal Jos, to wannna waliyyin Allahn ne, katibi ne na Shehu Malam Tijani, Radiyallu Anhum.

 

An rayu cikin hidimtawa Allah cikin kowanne lokaci, rayuwa ce tsakanin koyar da dukkan iliman zaure, ambaton Allah (Zikiri), nasiha ga Al-ummah da kuma mabiya Darikar Tijjaniyya muji tsaron Allah SWT a cikin ayyukan mu.

 

Allah ya jikan sa ya gafarta masa. Amiiiin

Share

Back to top button