Innalillah Wa’inna Ilaihir Raji’un: Allah Ya Yiwa Mai Martaba Hakimin Kwadwo Rasuwa Dake Jihar Gombe.

Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

 

…Masoyin Annabi Muhammadu SAW Ya Rasu.

 

Allah ya yiwa mai martaba Alhaji Muhammad Sani Abubukar Hakimin Kwadwo rasuwa dake karamar hukumar Yamaltu Deba jihar Gombe.

 

Muna mika sakon ta’aziyya ga daukacin al’ummar Musulmai musamman masoya Manzon Allah SAW tare da iyalai bisa rasuwa Masoyin mu mai martaba Alhaji Muhammad Sani Abubakar (Hakimin Kwadwo) dake karamar hukumar Yamaltu Deba jihar Gombe.

 

An gudanar da sallar jana’izan yau talata da misalin karfe 2:00pm na yamma a babban masallacin juma’a na Kwadon dake jihar Gombe.

 

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa, Allah ya karbi shahadar sa. Allah ya yafe masa. Amiiiin Yaa ALLAH.

 

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button