Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Allah Ya Yiwa Malam Abdullahi Dogon Diwani Dake Jihar Borno Rasuwa.

INNALILLAHI WA’INNA ILAHIR RAJI’UN

 

….BORNO TAYI BABBAN RASHI

 

A Jiya Talata 6/9/2023 Jihar Borno Tayi Rashin Ɗaya Daga Cikin Manyan Jagororinta Ɓangaren Makaranta Diwanin Yabon Sayyiduna RasululLahi SallalLahu AlaiHi Wa A’liHi Wa Sallama Na Maulan Mu Shehu Ibrahim Niass RTA Wato Ɗan Uwan Mu Cikin Allah Malam Abdullahi Dogon Diwani

 

Malam Abdullahi Dogon Diwani Mutumin Kirki Ne Salihi Mai Tsoron Ubangiji Wanda Ya Ƙarar Da Rayuwar Sa Cikin Bin Allah Da Manzonsa Da Ibada Da Riƙo Da Hannun Bayin Allah Zuwa Gare Su Da Dasa Soyayyar Shugaba SAW Da Son Yabon Sa A Cikin Zuƙatan Su Manyan Su Da Ƙananan Su.

 

Sannan Ɗayane Daga Cikin Muridai Khadimai Na Maulan Mu Shehu Abulfathi RTA Ƙarƙashin Kulawar Katibin Sa Sheikh Malam Salisu Baffa R.T.A

 

A Madadin Ni Kaina Da Iyalai Da Ƴan Uwa Muridai Da Membobin Ƙungiyar Mu TA Fityanul Islam Of Nigeria Reshen Babban Birnin Tarayya Abuja Ina Miƙa Ta’aziyyar Mu Ga Hadaran Maulan Mu Shehu Abulfathi RTA.

 

Da Katibin Sa Sheikh Salisu Baffa RTA Da Dukkanin Ƴaƴan Ta Na Rashin Wannan Babban Khadimi Kamar Yadda Nake Miƙata Ta’aziyyar Mu Ga Iyalansa Da Dukkanin Makaranta Diwani Na Jahar Borno Da Ma Najeriya Da Duniya Baki Ɗaya

 

Allah Ya Sada Shi Da Sayyiduna RasululLahi SAW Da Dukkanin Khalifofin Sa Baki Ɗaya Albarkar Maulan Mu Sheikh Ahmad Abulfathi Alhasany Alyarwawy RTA. Amiiiin

 

Daga: Al-Murabbi Al-barnawi

Share

Back to top button