Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un, Allah ya yiwa matar Sheikh Harisu Salihu Jos rasuwa.

Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un

 

….Allah Ya Karbi Rayuwar Mai Dakin Babban Malamin Addinin Musulunci A Najeriya.

 

ALLAH ya yiwa matar babban malamin addinin Musulunci kuma shehin Darikar Tijjaniyya Sheikh Dr, Haris Salihu (Kakakin Faila) Jos rasuwa a safiyar yau Lahadi.

 

Hajiya Sayyada Wasila (Aunty Inyass) itace babban a dakin Sheikh Harisu (shugaban hukumar alhazai na jihar Plateau).

 

An gudanar da Sallah JANA’IZA Ta kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar a kofar gidan Sheikh Harisu Salihu dake layin monedo garin Jos.

 

Allah ya jikan ta da rahma ya gafarta Mata, albarkan Annabi Muhammadu ﷺ. Amiiiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button