Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Allah Ya Yiwa Zakiru Yahya Ahlul Baiti Dake Lafia Rasuwa.

INNA LILLAHI…

 

ALLAH Ya Yiwa ZAKIRU YAHYA AHLUL-BAITI LAFIA Rasuwa Jiya Da Daddare, Hakika An Yi Babban Gi6i a Hidimar MANZON ALLAH (S.A.W) Da ZAKIRAI a ‘Kasar LAFIA, Hadimi Na Gasken-Gaske.

 

Za’a Yi Jana’izarsa Yau Da Misalin ‘Karfe 02:00 (Bayan Sallar Azahar) a Unguwar Rimi Uku Lafia, Jihar Nasarawa.

 

A Madadin Hukumar Gudanar Wa A Kamfani Tijjaniyya Media News Karkashin Jagoranci Babangida A Maina Tana Mika Sakon Ta’aziyya Ga Yan’uwa Da Iyalan Mamacin Allah Ya Bada Hakurin Wannan Rashi.

 

ALLAH Ya Jaddada Rahma a Gare Shi, Ya ‘Kara Masa Kusanci Ga SHUGABA (S.A.W), In Namu Lokacin Yayi, ALLAH Ya Kyautata Namu ‘Karshen, Ameeeeeen

 

Daga: Othman Muhammad

 

 

Share

Back to top button