Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un, Sarki Masoyin Manzon Allah SAW Ya Rasu A Jihar Gombe

Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

 

Allah ya karbi rayuwar daya daga cikin manyan sarakunan Musulunci kuma dan Tijjaniyya rasuwa a jihar Gombe.

 

Allah ya yiwa mai martaba sarkin Funakaye Alhaji Ma’azu Muhammad Kwairanga rasuwa.

 

Mai martaba sarkin Funakaye Alhaji Ma’azu Muhammad Kwairanga mutum ne mai hidimtawa addini Musulunci da tabbatar da gaskiya da adalci a rayuwar sa, matashi wanda ya sadaukar da rayuwar sa wurin taimakon al’ummar sa a koda yaushe.

 

Za’ayi gudanar da sallar jana’izan sa yau Lahadi 28/08/2022, da misalin karfe 2:00 na yamma a garin Bajuga karamar hukumar Funakaye jihar Gombe.

 

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa Allah ya jaddada masa rahma Amiin.

 

Babangida A Maina

National Director Fityanu Media

Share

Back to top button