Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Sayyidah Aisha mace ce mai tsananin kamun kai, duk da tana rayuwa ne cikin Ghetto.,

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN

 

Ɗaya daga cikin dalibai masu haddar diwani na makarantar Shehu Abulfathi dake Minna, ta rasu.

 

Nanah A’eeshat Bintu Ibrahim

 

Jiya aka gaya min tana emergency ward, da safen nan naji saqon wafatin ta.

 

Sayyidah Aisha mace ce mai tsananin kamun kai, duk da tana rayuwa ne cikin GHETTO, Amma kowa ya mata kyakkyawar shaida, musamman wurin neman ilimi, rashin hayaniya, girmama na gaba da ita.

 

Ni kaina, tana cikin daliban da nake alfahari dasu wurin himma tun yarintar ta, Ina daga cikin malaman ta a islamiyya, ni na bata darikar Tijjaniya, a hannu na take haddar diwani.

 

Allah alfarmar sunan ta, don kyakkyawar shaidar da akayi mata, don haddar diwanin da take kan yi, don mai makarantar da take ciki (Shehu Abulfathi), ka haskaka kabarin ta, kasa wafatin ta ya zama sanadin shiriya ga sauran al’umma, Alfarmar Annabi SAW.

✍️ Sid Sadauki.

Share

Back to top button