Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un Tijjanawa Na Jimamin Rashin Wani Matashin Dan Uwan Su

SAYYADI ƊAHIRU YAYI DACE DUNIYA DA LAHIRA.

 

ALLAH ya yiwa Sayyadi Dahir Abubukar DK dake karamar hukumar Dukku jihar Gombe rasuwa.

 

Irin wannan ƙarshe muke roƙo kullum, Allah ya bamu ikon cikawa da imani, kafin nan kuma ya albarkacemu da aikata aikin alkhairin da za’a tunamu dashi bayan macewarmu.

 

Wannan bawan Allah batijjanene ɗan uwana kuma ɗan faira na gaskiya ba shirme ba. Ban taɓa wata mu’amala dashi ba ko a Media sai dai sau tari mukanyi musafaha sakamakon haɗuwa cikin hidimar Allah.

 

Yau mun wayi gari ya koma ga Allah, tun safe kyakkyawar shaida kawai nake gani ake masa musamman ta soyayyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

 

Shi kam yayi dace, muma Allah yasa mu dace mu ciki da imani Albarkacin Shugaban Halitta Sallallahu Alaihi Wasallam. Amiiin

 

Mustapha Abubakar Kwaro

19/07/2022

Share

Back to top button