Inna’lillah Wa’inna Ilaihir Raji’un: Yan Bin@diga Sun Ka@she Mutane Hudu Tare Da Tafiya Da Wasu A Zaria

‘Yan Bindi#ga Sun Ka@she Mutane Hudu Tare Da Tafiya Da Wasu A Zaria.

 

…al’amuran tsa#ro a Arewa na cigaba da tabarbarewa

 

Rahotanni sun tabbatar da cewa a daren jiya Juma’a da misalin karfe 11na dare , masu gar$kuwa da mutane sun yi dirar mikiya a Anguwan Dankali yankin Dan Magaji dake Zaria.

 

Maharan sun je gidan Alh Musa, inda suka tafi da mata.

 

Maha@ran dai sun dinga har@bi ba kakkautawa ga wanda suka yi karo da shi. Inda aka tabbatar da sun kashe mutane hudu tare da ji wa wasu raunuka suna asibiti.

 

Ya zuwa safiyar nan an samu kiran waya daga matan da aka tafi da su cewa sun kubuta daga hannun masu gar@kuwa da mutanen amma ba su san inda suke ba.

 

Muna rokon Allah ya jikan wadanda suka rasu.

 

Ya kubutar da wadanda aka kama, sannan ya yi mana maganin ta’adda@nci da ‘yan ta@’adda.

 

Daga Abban Al’amin

Share

Back to top button