INNALILLAHI: Allah Yayiwa Sheikh Abubakar Wanda Akafi Sani Da (Malam Sidi) Bolari Rasuwa A Safiyar Yau Litinin.

INNA’LILLAHI WA’INNA ILAIHIR RA’JIUN😭

 

Allah Yayiwa Sheikh Abubakar Wanda Akafi Sani Da (Malam Sidi) Bolari Rasuwa A Safiyar Yau Litinin 2-01-2023.

 

Za’ayi Jana’izar Sa Ayau Insha Allahu A Ƙofar Gidansa Dake Bolari Wajen Masallachin Filin Ƙwallo, Arewa Da Layin Babban Dam Na Ruwa, Da Misalin Ƙarfe 02:30pm.

 

Shehu Malam Siddi Fitachchen Malami Ne Mai Matuƙar Tsantsaini Ga Tsoron Allah Ga Kuma Yawan Sallah Da Salatin Annabi Muhammadu S.a.w.

 

Baya Ga Haka Ya Kasanche Yana Bada Karatun Ilimin Addini A Lokuta Mabambanta A Chikin Yini Guda, Inda Dayawa Daga Chikin Manyan Malamai Da Sauran Bayin Allah Su Kanje Garesa Domin Ɗaukar Karatun Na Fannoni Da Dama.

 

Malam Siddi Chikakken Batijjane Ne Masoyin Manzon Allah S.a.w. Wanda Yanada Masallachi Inda Ake Karanta Wazifa, Sannan A Kowachche Shekara Akan Gabatar Da Maulidi A Ƙofar Gidansa Dake Nan Bolari.

 

Marigayin Yabi Bayan Iyalinsa/Matar Sa Wadda Itama Allah Yayiwa Rasuwa A Makon- Nan Daya Gabata.

 

Marigayiyar Tabar (Matar Sa) Ta Rasu Ta’ Bar Ya’ya’ Huɗu (4) Da Jikoki Talatin Da Sama (30+)

 

Allah Yamusu Rahma Baki Ɗaya 🤲

 

Muhammad Izzuddin Abubakarkar

Share

Back to top button