Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un: Allah Ya Yiwa Shahararren Malamin Musulunci A Najeriya Rasuwa Sheikh Dr, Yusuf Ali.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN 😭

 

Allah yayiwa shaharraren Malamin Addinin Musulunci da Ɗariƙar Tijjaniyya rasuwa Sheikh Dr. Yusuf Ali a daren jiya, kafin rasuwarsa ya kasance shine Sarkin Malam Gaya, Allah ya masa baiwa iri-iri ga kuma tarin ilimi wanda ya amfani ɗumbin al’umma.

 

Za’a masa sallah kamar yadda Addinin Muslunci ya tanadar yau Litinin 06/11/2023 da misalin ƙarfe 1:30pm na Rana in Allah ya kaimu a Masallacin Murtala Tudun Maliki.

 

Allah ya jiƙanshi ya gafarta masa. Amin

 

Mustapha Abubakar Kwaro

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button