Jawabin Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA A Zaben Shugaban Kasa Shekara Ta 2023.

HIKIMOMINE CIKIN FATAWOWIN GUDA BIYU, MADALLAH DA WANNAN JAGORA GWANIN ZAYYANA ADALCI A KALAMANSA.

 

 

Na lura dayawa wasu daga yan uwa sun shiga rudani, bayan sauraron zantukan sauti guda 2 daga Maulana Sheikh (R.T.A) game da matsayarsa akan wannan zabe, inda wasu suke ganin, kamar zancen farko na sabawa na biyunsa, da dai wasu al’amura makamanta haka.

 

A iya dan karanin nazari na, Ni banga abin daure kai ba cikin fatawowin Maulana Sheikh game da wannan zabe ba, domin bita daya nayiwa zancen na fahimceshi tarwai, ba tare da na sake bita ba.

 

1- Fatawa ta farko Maulana (R.T.A) yayitane ga Mujtama’a Duniyar (Tijjanawa) masoya akan kowa yaje ya zabi wanda ya kwanta masa a rai daga cikin yan takarkaru (Ko da Dan Jarida ya same shi), wannan fatawace da Maulana Sheikh ya sauke hakkin dake wuyansa a matsayinsa na uba kuma daya daga cikin jagororin Tijjanawa a Dunuya, kasancewarsa mai yawan hikima kuma ma’abocin adalci, sai ya baiwa kowa dama, tunda wannan sha’anine na Duniyarsu. Misali, kamar dai layin wayar Salulane da zaka tambayi Maulana Sheikh da wanne ya dace kayi amfani tsakanin MTN, AIRTEL, ko GLO, to zaice dakai kaje kayi amfani da wanda ya kwanta maka a rai, to haka suma yan takarar dake dukkan jam’iyyu.

 

2- Fatawa ta biyu kuma da zamu lura Maulana Sheikh yayi amfani da kalma Muqayyada, wato makusanta wasu (Daga Family) sun sameshi da wanda suke so su zaba wanda shine Atiku, (Kasancewar su masu matukar ladabi da biyayya gareshi, basu son aikata abinda babu umarninsa ciki wanda hakan shine dalilinsu na zuwa gareshi) shi kuma a matsayinsa na uba mai yawan adalci da sakarwa kowa mara akan abinda babu sabon ALLAH cikinsa, sai yace da su shikenan suje su zabi Atikun harma domin kara girmamasu saboda hikima sai yayi amfani da kalma “gamayya” mu Wato dai Misali kamar suce sunason Amfani da layin MTN daga barin waninsa, kaga bazaice musu a’a ba.

 

Sam-sam a fahintata zancen Maulana Sheikh na farko bai sabawa na biyu ba, sannan kuma zancen karshen bai kore na farkon domin baice kada a zabi wani dan takara sabanin Atiku ba, baldai kowanne da nasa matsayin gwargwadon wadanda akayi zuwa garesu, kuma wannan dama shine cika ta kamala irin na bayin ALLAH suna zance da kowa gwargwadon matsayi da kusancin dake tsakaninsu.

 

YA ALLAH A KARA KULAWA DA SHA’ANIN WANNAN WALIYIN, A KARA MASA JURIYA DA HAKURI DA LAMARIN YAN ZAMANI, A KARA TSARE MASA MUTUMCI ALFARMAR MANZON ALLAH (S.A.W). AMIIN YAA ALLAH.

 

Daga: Muhammad Usman Gashua

Share

Back to top button