Jirgin Sojojin Saman Najeriya Sun Harbo Bom Ga Masoya Manzon Allah SAW Dake Taron Mauludi A Kaduna.

Innalillahi Wa’inna Ilaihir Raji’un 😭😭

 

…. Kungiyar Darikar Tijjaniyya Ta Fityanul Islam Initiative Ta Kasa Tana Allah Wadai Da Abunda Rundunar Sojojin Saman Najeriya Su Kayi.

 

A daren jiya lahadi ne 03/12/2023, Rundunar sojojin saman na najeriya sun harbo Bom akan masu murnan Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ a garin Tudun/Biri dake karamar hukumar Igabi jihar Kaduna wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 50.

 

Muna kira da babban murya ga gwamnatin jihar Kaduna da rundunar sojojin kasan najeriya dasu binciki wannan al’amari tare da biyan diyya wanda suka rasa iyalan su baki daya.

 

Daga karshe muna kira da yan’uwa Musulmai dasu kwantar da hankalin su akan al’alamari.

 

Ubangiji madaukakin sarki ya jikan su da rahma ya gafarta masa, Allah ya karbi shahadar su. Amiiiin Yaa ALLAH

 

Daga: Babangida Alhaji Maina

Fityanu Initiative Media

Share

Back to top button