Kadan Daga Cikin Littattafan Da Maulanmu Shehu Atiku Sanka Ya Rubuta.

Kadan Daga Cikin Littattafan Da Maulanmu Shehu Atiku Sanka Ya Rubuta

 

Ya rubuta litattafai da dama, ga wasu daga ciki:

 

1) Majmu’i mai kundi 14, da aka hade kananan ayyukansa irinsu Ifadat al Murid, Futuhatul Mannan, Raf al I’itirad, al Fuyudat da sauransu.

 

2) Abyatul Rakika, akan murnar ziyarar da malaminsa al Hajj bin Umar ya kawo Kano.

 

3) Asl Ammani akan mata muqaddimai.

 

4) Badhl Nada akan kasidar Ishiriniya.

 

5) Fathal Ahad akan wadanda suka yi shahada a yakin Uhud.

 

6) al Fathal nurani akan wuridin Tijjaniyya.

 

7) al Faydal Ahami akan tarihin manyan malaman dariqar Tijjaniyya.

 

8) al Anat al Bulada akan koyan luggar larabci.

 

9) Irsalat al A’inna akan tarihin sarakunan Katsina.

 

10) Irshadal al Ahibba akan haramcin shan taba.

 

11) Manahil al Rashd amsa ga wasu fatawoyi da akayi masa daga kasar Chad.

 

12) al Sarim al Mashrafi wani raddi da ya yiwa Shehi Malam Nasiru Kabara. Akan wani littafi na Malam Nasiru maisuna Nafhatil Nasiriyya.

 

13 Tanbihan Nubaha akan ko za’a iya ganin

Manzon Allah (SAW) a farke. Ya kawo hadisai da suka nuna hakan a cikin wannan kasida.

 

14) Aybatal Fukara qasidar Hausa akan  Shehi Ahmad Tijjani.

 

15) Munjiyat an Niswan akan matsayin mata a Musulunci.

 

16 ) Raka Dua ita ma wakar Hausa ce akan yadda zaka koyi luggar larabci.

 

An tabbatar da Malam Atiku ya rubuta sama da litattafai sittin a rayuwarsa.

 

Allah Ya Jikan Sa Da Rahma, Allah Ya Sadashi Da Babban Masoyin SA. Amiiiin

 

🖋Usman Yahaya Sufi

Share

Back to top button