Kafin fara “Yakin” Karbala, Imam Husain (RA) ya tsaya a gaban sojojin Yazid don kafa musu hujja su san da wa suke yaki, inda ya ce musu:

Kafin fara “Yakin” Karbala, Imam Husain (RA) ya tsaya a gaban sojojin Yazid don kafa musu hujja su san da wa suke yaki, inda ya ce musu:

 

“ku duba da kyau ku ga ko ni wane ne sannan ku koma ga zukatanku ku tambayesu shin ya halalta gare ku ku kashe ni da kuma keta mutumcina? Ashe ni ba dan ‘Yar Manzon ku (SAW) ba ne kuma dan wasiyyinsa kuma dan baffansa, wanda ya fara imani da Allah da kuma gaskata Manzon Sa ba?

 

Ashe Hamza shugaban shahidai ba baffan babana ba ne? Ashe Ja’afar al-Tayyar ba baffana ba ne? Ashe kalamin Manzon Allah (SAW) dangane da ni da dan’uwana bai iso gare ku ba, inda yake cewa:

 

‘Wadannan guda biyu su ne shuwagabannin samarukan aljanna? To idan har kun gaskata ni kan abin da na ce – kuma hakan ita ce gaskiya- wallahi ban taba ganganta yin karya ba tun daga lokacin da na san cewa Allah zai azabtar da ma’abucinta.

 

Idan kuwa kun karyata ni to cikinku akwai wanda idan kuka tambaya shima kan hakan zai gaya muku, ku tambayi Jabir bn Abdullah al-Ansari, ko kuma Abu Sa’id al-Khudri ko kuma Sahl bn Sa’ad al-Sa’idi, ko kuma Zaid bn Arkam ko kuma Anas bn Malik , za su tabbatar muku lalle sun ji Manzon Allah (SAW) yana fadin wannan zance a kaina da dan’uwana.

 

Ashe wannan ba zai kasance muku shamaki wajen zubar da jinina ba?

 

Sai Husaini (RA) ya ci gaba da cewa:

 

“Idan har kuna shakku ne kan wannan abin da na fadi ko kuma kan cewa ni dan ‘yar Manzonku ne, to wallahi babu wani dan ‘yar Annabi a bayan kasa daga cikin ku ko kuma da cikin wasunku in ba ni ba. Ni ne kawai dan ‘Yar Manzonku, ku gaya min shin kuna neman fansar jinin wani ne da na kashe daga cikinku? Ko kuma wata dukiya taku da na cinye? Ko kuma fansar wata cuta da na yi wa wani”

Share

Back to top button