Kalaman Gwamnan Borno A Wurin Maulidi Manzon Allah SAW A Zawiyyan Sheikh Ibrahim Sale Maiduguri.

MAULUD DAGA MAIDUGURI
Zaman Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ Wanda Aka Gudanar A Zawiyyan Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al Hussaini (Shugaban Masu Fatwa A Najeriya) Dake Birnin Maiduguri Jihar Borno.
Gwamnan Jihar Borno Prof Babagana Umara Zulum Tare Da Tawagar Sa Sun Samu Halartan Mauludin Da Kuma Dubban Jama’a Masoya Daga Sassan Duniya.
A Cikin Jawabin Prof, Babagana Umara Zulum Gwamnan Jihar Borno Ya Bayyana Cewa Ya Zama Wajibi Duk Wani Musulmi Mai Kishin Addinin Sa Da Kuma Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ Yaso Annabi SAW.
Ya Kara Cewa Soyayyan MANZON ALLAH SAW Wajibi Ne, Kuma Yana Kira Ga Daukacin Al’ummar Musulmi Na Kowanne Bangare Mu Dage Da Addu’o’i Zaman Lafiya A Ko’ina A Fadin Najeriya Musamma Jihar Borno.
ALLAH Ya Maimaita Mana Ya Kara Mana Soyayyan Annabi Muhammadu SAW. Amiin
Babangida A Maina