Kallin Yadda Wani Matashi Ya Rubuta Alkur’ani Mai Girma Da Hannun Sa.

BABBAN KUNDI, DUK WANDA YA DAUKEKA A “KA” YAFI KARFIN RAINI.

 

Ziyara kenan da na kaiwa dan uwa Assayyid Alhaji Muhammad Bako tare da sanya albarka ga namijin aikin da ya aiwatar na kammala rubuta Al-Kur’ani mai girma.

 

Babbu shakka, kowa ana jinjina masa akan kokarinsa, gwargwadon matsayi da darajar abinda yayi hidima akai, amma lallaine babu wadanda suka chanchanci madaukakiyar jinjina sama da wadanda suke dauke da mafi girman littafin ALLAH, sannan kuma mafi girman mu’ujizar MANZON ALLAH (S.A.W) a zukatansu, kamar MAHADDATA ALKUR’ANI, domin su din sun kasance zababbune cikin dubbai, ALLAH ke tantancewa tare da adana littafinsa a Kirazansu.

 

Lallai tsangaya ta kasance bakar tukunya (A idanun yan zamani) amma abincin da take dafawa shine mafi darajar abinci da ke gusar da yunwar Addini, har ta samu kuzarin wanzuwa da tsayuwa tsawon zamani.

 

ALLAH KA ALBARKACEMU DA ALBARKAR MAHADDATA AL-KUR’ANI. AMIIN

 

Muhammad Usman Gashua.

Share

Back to top button