Karanta Alqur’ani Yafi Karanta Salatul Fatih, Wannan Maganar Na Rubuce A Cikin Littafin Jawahirul Ma’ani
Karanta Alqur’ani Yafi Karanta Salatul Fatih, Wannan Maganar Na Rubuce A Cikin Littafin Jawahirul Ma’ani
…..Cewar Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zariya
Babu wani dan tijjaniyyan da yarda cewa Salatul Fatih tafi Alqur’ani, domin Shehu Tijjani da almajirasa basu fadi haka ba, kuma a littafin Jawahirul Ma’ani cewa aka yi karatun Alqur’ani yafi wuridin tijjaniyya da kowace irin wuridi idan mai karanta ta ya kiyaye haddodin ta. Shiyasa mu ‘yan tijjaniyya ba mu da wani littafin da muka rike fiye da Alqur’ani, kuma mu ‘yan tijjaniyya munfi kowa yawan mahaddata Alqur’ani musamman a nan Najeriya.
Masu cewa ‘yan darika sunce Salatul Faith tafi Alqur’ani shashashai ne, makaryata ne, masharranta ne, ba wani abu yasa suke fadan haka ba illa yunkurin dusashe hasken tijjaniyya a wajen wawaye, amma hakansu bata cimma ruwa ba saboda Allah yana cewa :
يريدون أن يطفئوا نور الله بأفواههم ويأبى الله إلا أن يتم نوره،
~ Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria