KAREWA/FARAWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1443/1444 TAMBAYAYOYI DA ZAMU AMSA.

KAREWA/FARAWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1443/1444@H TAMBAYAYOYI DA ZAMU AMSA.

 

Kamar jiya, muke bankwana da 1442 da Murna Zuwan 1443@H yau gashi cikin ikon Allah ta Kare kuma 1444 zata fara. Alhamdulillah

 

Sai dai wannan abin kuka ne da murna a lokaci daya, domin karewar dare da wuni, da karewar mako da wata zuwa karewar shekara

 

Hakika abin lura ne dake nuna mana da tabbata mana karewar rayuwar mu ta duniya, da ita kanta duniyar zuwa gidan matabbaci lahira

 

Kawai abin da zai sa muyi MURNAR zagawowa shekara shine idanln muka Kalli cewa yana kara bamu damar shedar ibadu masu lokutta

 

Kamar Zakka, Azumi, Hajji, Umra, bayan Kuma Sallollin Farilla da Nafiloli tare da sauran ibadu Masu kayyadaddun lokutta na Musamman

 

A dayan 6angaren abinda zamu tuna muyi kuka shi ne, ba shakka ajalin mu na karewa Muna kara Nisa da duniya Muna kara kusantar Qabri

 

Kuma Wannan ba shakka, ba Canzawa Kuma ba fasawa mun shirya ko bamu shirya ba, idan Kuma LOKACIN yazo ba’a saurarawa kowa

 

Shi Allah Ta’alah daya Haliccemu ya sanar damu Dalililn Halittar mu don mu bauta maSa, a Maganarmu da Aiyukanmu da Halayenmu

 

A: Tambayar itace;

 

1 Duk abinda Allah yayi horo mun aikata?

2. Idan mun aikata munyi yadda yacce?

3. Idan munyi yadda yacce munyi don Shi?

4. Idan munyi don Shi ya kar6a?

5. Idan bai kar6a ba, ya kenan?

 

B: Dangane da sa6o kuwa ko Zunubi:

 

1. Duk abin da Allah ya Hana mun bari?

2. Idan mun yi Zunubai Muna Tuba?

3. Idan munyi Tubar munayin ta gaskiya?

4. Idan munyi ta gaskiyar Allah ya kar6a?

5. Idan bai kar6a ba, ya kenan?

 

Subhanalllah, Astagfirullah, Walahaula Wala Quwwata illah billah, na tabbata duk Mai Imani Wannan tunani zai girgiza shi, Kila har da KUKA

 

To Ina abin yi, Meye Mafita?

 

Domin kuwa Nabbata ba Wani Musulmi da zaiyi Karfin HALIN cewar duk abin da Allah yayi horo ya aikata, ko duk abin da aka Hana yabari

 

Kenan abin da ya Wajaba gaba dayanmu mu, sai mu kar6a Kiran Allah daya ke cewar: “Ku tuba gaba dai yaku Masu Imani don Ku rabauta

 

Kuma Sharuddan Tuba Uku; kamar yadda suke

 

1. Nadama akan abin da ya wuce (Na Laifi)

2. Niyar bazaka sake aikata laifin ba

3. Barin laifin nan take, Kar kace sai lokaci kaza

 

Wannan idan laifin tsakaninka da Allah ne, idan Kuma akwai hakkin dan Adam Wajibi ne, Mayar da hakkin ga mai shi ko neman yafewarsa

 

Idan akayi tuba ingantacce, Allah ya na Murna Kuma yayi Alkawalin Gafartawa, har ma yakan Maida Zunubi Lada, idan TUBA yayi kyau

 

Kuma ita kadai ce, hanyar da zamu iya riskar abinda ya wuce na ba daidai ba, tare da rokon Allah ya kar6a dan abinda Muka yi daidai don Rahmarsa da FalalarSa da Albarkar Annabi saw

 

Muna kara godewa Allah daya sake nuna mana karewar Shekarar 1443, Muna rokon Allah yasa Muga karshen 1444 cikin cikar Imani da Lafiya

 

Allah yasa Muna cikin masu samun daukaka da wadata da ilmi da karin lmani da koyi da Annabi saw a cikin komi, Yasa mu cika da Imani duk lokacin da Karshen mu yazo. Ameen

 

سبحانك اللهم و بحمدك أشهد أن لا إله أنت أستغفرك وأتوب إليك الاهم صل على سيدنا محمد صلاة تعرفنا بها إياه .

 

Abdulhakeem Ahmad Ya’akub Gusau 20/07/22

Share

Back to top button