KARSHEN YANCIN DAI RAHAMAR ANNABI (S.A.W) DA TAUSAYINSA GA MUTANE.
KARSHEN YANCIN DAI RAHAMAR ANNABI (S.A.W) DA TAUSAYINSA GA MUTANE….
Limamin Masallacin Abuja Maulana Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari Hafizalullah yana cewa;
Lokacin da cutarwa ya tsananta ga Annabi bayan rasuwar Abu-dalib da Khadija (R.A) ; Annabi sai ya fita daga Makka ya nufi garin da’if, anan ne ya kira kabilar Sakiif i zuwa ga musulunci.
Sai dai kash ! hako bai cimma ruwa ba, domin kuwa basu tari Annabi da komai ba in banda cutarwa mai tsanana da izgilanci da taurin kai, har ya kai ga cewa sun jejjefe shi da duwatsu suka ji masa rauni a kafafuwarsa, daga karshe Annabi sai ya yanke shawarar dawowa garin Makka.
Annabi yace : “Na kamo hanyar dawowa daga da’if ina cike da bakin ciki, ban fadaka ba har sanda na zo gurin da ake kira karnus-sa’alib (mikatin mutanen Najd), ina daga kaina sai ga wani girgije yamin inuwa, dana duba sai naga ashe mala’ika Jibril ne a ciki.
Sai ya kira ni yace : hakika Allah yaji abin da mutanen ka suka gaya maka, da kuma martanin da sukayi maka, yanzu haka Allah ya aiko maka da mala’ikan dake rike da duwatsu ne don ka umarce shi da duk abin da kaso ayi dasu. Sannan sai mala’ikan dake rike da duwatsu ya kira ni ya min sallama yace :
Ya Muhammad ! hakika Allah yaji maganar da mutanenka suka maka, kuma nine mala’ikan dake rike da duwatsu, Allah ya turoni ne don ka umarce ni da duk abin da kaso, in kaso yanzu sai in kifar da wadannan manyan duwatsun a kansu ?
Sai Annabi yace :a’a kada ayi musu haka, sai dai ina fatar Allah zai fitar daga tsatsonsu wadanda zasu bauta wa Allah shi kadai kuma bazasu masa tarayya da komai ba.
[Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi].
Kuma Annabi ya kasance yana fita a mausimi (duk lokacin da za’ayi wani taro na musamman don ya bijirar da da’awarsa ga kabilun larabawa yana cewa :Waye zai bani mafaka ?.
Waye zai taimake ni ? domin kuraishawa sun hana ni isar da sakon ubangijina !.
Sallah’Lahu’alaihi Wa’alihi Wasallam. Maulana Allah Ya kara Lfy da imani da Mahabba
Allah Ya kara mana Son Annabi Sallah’ Lahu’alaihi Wa’alihi Wasallam. Amiiiin