Kaunar ANNABI Addini ne, so da kaunar ahlin gidansa, da sababbansa, da duk wanda yake biyayya ko koyi da abin da ya bari.

SON ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA IMANI NE.

 

Kaunar ANNABI Addini ne, so da kaunar ahlin gidansa, da sababbansa, da duk wanda yake biyayya ko koyi da abin da ya bari.

 

Duk wanda babu soyayyar ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA a ransa ko Yaji soyayyar wani tafi ta ANNABI a ransa, To Ya binciki imanin sa.

 

A cikin Hadisai Guda 2 ANNABI ya sanar da mu. “Babu dayan ku da zai zama yana da imani

 

Sai ya zamo yafi kauna ta fiye da kansa, mahaifinsa/mahaifiyar sa, Ko dansa/’yarsa da sauran mutane.”

 

Mutane sun hada da malaminka/oganka/ mai kula da kai, ko wanda ya ke ba ka kariya cikin mutane in ka shiga kunci ko damuwa.

 

Muyi koyi da ayyukan ANNABI da maganganun sa, Duk wanda ya saba da Umarnin da ANNABI (S.A.W) ya bayar, ko waye! kabi ANNABI ka kyaleshi.

 

Muyi tutiya da son ANNABI (S.A.W) kuma ku bayyana shi a ko ina, a ko da Yaushe.

 

Domin yafi kaunar da mu ke tutiya da ita ta matan mu, iyayenmu, ‘Ya’yanmu, da Makusantan mu.

 

Yin salati ga Annabi yana cikin kauna da soyayyar sa.

 

Mu yawaita salati gareshi.

 

Allah ya kara mana son ANNABI SALLALLAAHU ALAIHI WASALLAMA. Amin.

Share

Back to top button