Khalifofin Shehu Ibrahim Inyass RA A Najeriya Wadanda Shehu Ya Basu Muqadamanci Da Hannun Sa.

Halifofin Shehu Ibrahim Inyass RA A Najeriya Wadanda Shehu Ya Basu Muqadamanci Da Hannunsa

 

Rayyahi Sani Khalifa

 

Akwai wasu daga cikin halifofin Shehu a Najeriya wadanda Allah yayi musu baiwa da samun mukadamanci kai tsaye daga hannun Shehu RA, kamar yanda na samu a cikin littafin ( رجال وادوار حول صاحب الفيضة ) wanda Sheikh Muhammad dan Shehu Abdullahi Altijani ya rubuta. A cikin wannan littafin mawallafin ya tattara sunaye da takaitattun bayanai akan kowani Shehi, da kuma ainihin wasiqar/shahadar da Shehu ya rubutawa kowanni daya daga cikinsu na mukaddamanci. Wadannan shehunnai su ke da izini mudlaqi na bada darika da mukadamanci da bada izinin karanta asraran tijjaniyya ga wanda suka ga dama a kuma lokacin da suka ga dama daga wajen Shehu RTA. Wadannan dai sune tushen Faidha a Najeriya dan haka muridai da sauran al’umma ku sani cewa duk wani abu da ake danganta shi da faidha idan bai fito daga wadannan zawiyoyin ba ko rasan da suka haifar to da’awa ce kawai ba darikar tijjaniya bace, dan haka na nakalto domin muridai su san inda ya kamta ya zamo mashayansu, saboda masu da’awa da Shehunnan bogi marasa asali wadanda suke raba mutane da Allah da Annabi SAW da Shehu sunyi yawa a wannan zamani.

 

Ga sunayen Shehunnan da jihohin da suka fito :-

 

*Jihar Kano

01. Sarkin Kano Abdullahi Bayero RA

02. Sarkin Kano Khalifa Sunusi RA

03. Shehu Atiku Sanka RA

04. Shehu Tijjani Na Yan Mota RA

05. Shehu Sani Kafanga RA

06. Sheikh Mahmud Salga RA

07. Sheikh Faruk Abdullahi Salga RA

08. Sheikh Malam Abdullahi Salga RA

09. Shehu Usman Maihula RA

10. Sayyadi Alhaji Mahmud Dan Gwago RA

11. Muhammdul Khamis Ibnu Shu’aibu RA

12. Sharif Sheikh Ahmadu Al’ Anwar RA

13. Shehu Ishaqa Rabi’u RA

14. Shehu Dan Almajiri RA

15. Shehu Haruna Rashid Fage RA

 

*Jihar Kaduna

01. Shehu Malam Yahuza Zaria RA

02. Shehu Abdulkadir Zaria RA

03. Shehu Mu’azu Tudun Wada Zaria RA

04. Sheikh Tijjani Khalifa Abdulkadir Zaria RA

05. Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaia RA

06. Sheikh Malam Rabi’u Tudun Wada RA

07. sheikh Lawal Bara’u Kaduna RA

08. Sheikh Muhammad Inuwa Aliyu Zaria RA

 

*Jihar Katsina

01. Shehu Ja’afaru Katsina RA

02. Shehu Abdullahi Dandume RA

 

*Jihar Yobe

01. Shehu Gibrima Nguru RA

 

*Jihar Bauchi

01. Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA

02. Sheikh Aminu Bauchi RA

03. Shehu Adamu Azare RA

04. Sayyadi Muhammadul Hafiz dan Shehu Adamu Azare RA

05. Sayyadi Ali Ibnu Sa’eed RA

 

*Jihar Borno

01. Sheikh AbulFathi RA

02. Sheikh Sharif Ibrahim Saleh RA

3. Shehu Ahmad Tijjani Albarakawi RA

 

* Jihar Gombe

01. Shehu Adamu Manzo RA

02. Shehu Moddibo Ahmad Tijjani RA

03. Sayyadi Ibrahim Ibnu Hassan RA

04. Sayyadi Ibrahim Abdulkadir Bogu RA

05. Shehu Ahmad Bolari RA

06. Sayyadi Malam Hamid Usman RA

07. Malam Adamu Muhammad Chillo RA

08. Malam Ibrahim Ahmad Sarujy RA

 

*Jihar Adamawa

01 Shehu Modibbo Jailani Yola RA

02. Sayyadi Muhammadu Jada RA

03. Shehu Modibbo Suleiman RA

04. Sayyadi Muhammad Umar RA

05. Sayyadi Alkali Ahmad RA

06. Sayyadi Tahir Alkali Ahmad RA

07. Sayyadi Murtala Alkali Ahmad RA

 

*Jihar Plateu

01. Shehu Ibrahim Mushadid Jos RA

02. Shehu Abubakar Muhammad Alfulani RA

 

* Jihar Neja

01. Shehu Idris Fogun Bida RA

02. Shehu Umar Na Gusau Kontagora RA

03. Sheikh Ahmad Umar RA

04. Shehu Adamu Umar RA

05. Shehu Muhammad Umar Kontagora RA

06. Shehu Ahmadu Wushishi RA

07. Shehu Umar Mika’il RA

 

*Jihar Kogi

01. Sayyadi Abdulmalik Ibrahim Atta RA

02. Sayyadi Ahmad Alrufa’i RA

03. Sayyadi Ibrahim Dindi RA

 

*Jihar Lagos

01. Sharif Abdulmajid Muhammad RA

02. Sheikh Isma’il Ibrahim RA

03. Sayyadi Muhammad Ainla Lagos RA

04. Shehu Abubakar Muhammad Danial RA

 

*Jihar Ebonyi

01. Sheikh Ibrahim Nwagui RA

 

* Jihar Sokoto

01. Shehu Abubakar Malam Yabo RA

02. Shehu Muhammadu Aminu Masranu RA

03. Sayyadi Muhammad Dahir Masranu RA

 

* Jihar Zamfara

01. Shehu Balarabe Gusau RA

02. Shehu Ibrahim Alkali RA

03. Alhaji Ibrahim Kaya RA

 

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button