‘KISSA; An Yi Wani Bawan ALLAH a Zamanin Can Baya Ya Kasance Yana Bautar ALLAH (S.W.T) Har Na Tsawon Shekaru 600, Acan Bayan Gari Shi Kadai.

‘KISSA; An Yi Wani Bawan ALLAH a Zamanin Can Baya Ya Kasance Yana Bautar ALLAH(S.W.T) Har Na Tsawon Shekaru 600, Acan Bayan Gari Shi Kadai,

 

ALLAH Cikin Buwayarsa Ya Hore Masa Wata Idanuwar Ruwa Mai Gudana, Da Kuma Wata Itaciyar Inabi Wanda Kullum Zai Samu Guda ‘Daya Ya Ci Shi Ne Abincinsa.

 

Bayan Da Ya Rasu Sai UBANGIJI Ya Ce:”Ku Shigar Da Shi Aljanna Saboda Falala Ta Da Rahamaniyya Ta”,

 

Sai Wannan Bawan Ya Ce:”Ya UBANGIJI! Haba Saboda Aiki Na Dai Da Kuma Bautar Da Na Yi Maka Na Shekaru 600″,

 

UBANGIJI(S.W.T) Ya Ce Masa:”Ai Bautan Da Ka Yi Mini Bai Kai Darajar Ni’ima ‘Daya Da Nayi Maka Ba,

 

Na Kai Ka Daji Na Sanya ‘Korama Kana Amfana Da Ita, Bayan Cikin Gari Mutane Na Zaune Ban Basu Ruwa Ba,

 

Na Baka Inabi Kullum Sai Ta Tsiro Maka Da ‘Dan Itaciya Ka Ci, Bayan a Al’ada Sai Shekara-Shekara Take Yin ‘Yaya,

 

Na Baka Lafiyar Yin Bauta, Sannan Na Hana Shaid’an Zuwa Inda Kake, Don Zan Iya Barinsa Ya Sace Imaninka,

 

Duk Wannan Ni’imar Baka Gani Ba Sai Aikinka, Mala’iku Ku Kama Shi Ku Jefa Shi a Wuta”,

 

Sai Ya Ce:”Ya UBANGIJI Na TUBA Ka Sanya Ni Aljanna Don Rahamarka Da Falalarka”,

 

ALLAH(S.W.T) Mai Rahama Da Jinkai Ya Ce:”Ku Kai Shi Aljanna Don Rahamata”.

 

(SOURCE; Akhrajahu Mubarak Fi Masnadihi, Ibreez Min Qalami Abdul Azeez, Shafi Na 349).

 

*. DARASI:

 

Hikimar Wannan ‘Kissar Anan Shi Ne; Babu Wanda Zai Shiga Aljanna Sai Da Falala Da Rahamar UBANGIJI(S.W.T),

 

Mutum Ya Zama Bawan ALLAH Tsantsa(Ba Lebura Ba), Ba Bawan Ibadarsa Ba, Ko Shekara Nawa Ka Yi Kana Ibada Idan Dai An Tsaya Hisabin Aikinka Ba Zaka Sha Ba, Ka Godewa ALLAH Da Ni’imomin Da Ya Baka Na Kasancewa Musulmi.

 

ALLAH YA SA MU CIKA DA IMANI, KA YARDA DA MU DON RAHAMARKA BA DON HALIN MU BA YA ALLAH, AMEEEEN

Share

Back to top button