KISSA; Haduwar Sheikh Ibrahim Inyass RA, Tare Da Likatan As Mr, Z.Y A London.

‘KISSA: Lokacin Da SHEHU IBRAHIM NIASSE (R.A) Ya Je Asibiti a London, Sai Likitansa Wai Shi, Mr. R.Y. Ya Zo Yayi Masa Allura Da Idan Har Aka Yiwa Mutum Zai Yi Bacci Ne Na Awanni Bakwai Alal Akalli,

 

Bayan Fitar Likita Da Awanni Biyu Kacal Sai Ya Jiyo Karatun Al’Qur’ani a ‘Dakin SHEHU(R.A),

 

Sai Ya Fara Yiwa Shehu Hassan Cisse (R.A) Fada Don Me Suka Bar Wani Ya Shiga ‘Dakin SHEHU Zai Hana Shi Bacci???

 

Sai Suka Nufo ‘Dakin, Ga Mamakinsu SHEHU(R.A) Ne Yake Karatun Al’Qur’ani,

 

Sai Likitan Ya Fara Fargabar Wani Abu Mummuna Na Iya Samun SHEHU Don Haka Ya Ce:

 

Lallai SHEHU Ya Samu Ya Koma Yayi Bacci, Sai SHEHU(R.A) Ya Ce Da Imam Hassan Cisse (R.A):

 

“Ka Gayawa Likita Cewa Ni Tunda Na Cika Shekaru 30 a Duniya Na Ga Awa 24 Sun Min ‘Kadan Na Yi Duk Ayyukan Da Nake So, Don Haka Na ‘Dorawa Kaina Cewa Baccin Awa Biyu Kawai Zan Riqa Yi a Kullum”.

 

(Daga; Littafin Imam Nasir Adam Mai Suna:

 

الشيخ إبراهيم إنياس الداعية العالمي.

 

Shafi Na; 105).

 

SHEHU(R.A) Kenan!!!

 

Himma Bata Ire-Irenmu Ragwaye Ba!!!

 

(©️Dr. Tahir Lawan Muaz Attijany ✍️)

 

Barhama Kenan, Masani Na Rabbani!

 

Ya ALLAH! Ka Barmu Da’iman Da Soyayyar Masoyan MANZONKA(S.A.W),

 

Ya ALLAH Ka ‘Kara Nutsar Damu Cikin Ambaton MANZON ALLAH(S.A.W), Amiin

 

Allahumma Ameeeeen.

Share

Back to top button