KISSA; Kissar Manzon Allah SAW Da Wata Barewa Tare Da Makiyayi.

ANNABI S.A.W DA WATA BAREWA

(Daga Ƙissosin Mamaki Da Ban Ƙaye)

 

An Ruwaito wata rana Annabi (s) ya fita wani waje A Makka, Waje ne Da ya Shahara da Farautar Saboda Yawan Barewa da Tsuntsaye Dake Gun.

 

Sai Kwatsam Annabi (s) Ya Riski Wata Barewa A Tukuykuye cikin Igiya, Barewa Tana Ganin Annabi (s) Sai Taji Daɗi Tace “Ya Manzon Allah, Kaga Ga Wani Bayahude ya Kamoni, Alhali na Fito Kiwo ne dan Na Samu na Ciyar da Ya’yana, MANZON ALLAH INA ROKONKA KA FANSHE NI, IN NAJE NA SHAYAR DA YA’YANA ZAN DAWO GARESHI YA TAFI DANI” Sai Annabi (s) yai Murmushinsan nan Na Tausayi da Rahma, Yace “Kwantar da Hankali Zaki Kuɓuta inna bukaci ya Sakeki koya yarda ko bai yarda ba”

 

Sai Ga Bayahude ya Dawo Ya Tarar Annabi A Wajen Abun Farautarsa sai Yace “Me kike a Wajen Barewata?” Annabi (s) Ya Labarta masa sannan ya bukaci ya Sake Barewar shi zai Fanshe ta da Duk abunda Bayahude keso na Kuɗi.

 

Bayahude yace Sam! Barewarsa bata Sayarwa bane, Annabi (S.A.W) yace “Toh wannan Barewa ta Fito Kiwo ne dan ta ciyar da Ya’yanta kanana, yanzu tana Roƙo ka saketa taje ta Shayar da Ya’yan, tayi Alƙawari dasun Ƙoshi Zata Dawo insha Allah”

 

Bayahude ya Tuntsure da Dariya yace “Ka Taɓa ga Inda aka saki Barewa Ta gu kuma ta dawo? Wane Wasa da hankali ne wannan” Annabi (S) yace “Tamun Alƙawari lallai zata dawo” sai Bayahude yace “A’a Sai dai in kai zan Daure a Tarkon in bata dawo ba in tafi dakai a madadinta?”.

 

Annabi (S.A.W) yai Murmushi yace Na Amince, a take ya Miƙa hannayensa masu Albarka aka Ɗaureshi a madadin Barewa. Ita kuwa Baiwar Allahn ta falla da gudu cikin Daji.

 

Allah Mai Iko Yayin da Barewa taje da gudu ga Ya’yanta ta Faɗa musu Suyi sauri susha Zata Koma, Domin Annabi (S.A.W) aka Fansa a madadinta, Sai Ya’yan duk suka ƙi sha, suka ce Nononki ya haramta mana In har Sanda aka daure Annabi matsayin fansa. Allahu Akbar!

 

Barewa tai-tai su sha suka Ƙi, Sai ta Dawo wajen Annabi(s), Yayin da ta iso sai Bayahude yaga Annabi(s) Ya Fashe da matsanancin kuka, Bayahuden nan yai Mamaki sosai yace “Me kuma ya saka kuka Bayan Ga Barewar ta Dawo? Sai Annabi yace tazo ta Faɗa mun ne “Ya’yanta sunƙi shan Nonon saboda Ni aka daure a madadin hakan” La’ilaha Illallah!.

 

Nan Take Bayahude ya Fashe da kuka bisa ganin wannan Al’amari mai Girma Da Taɓa Zuciya, Nan Take ya Kurma Ihu yace “Fadaituka Ya Rasulallah!(Fansar Rai na Gareka ya Manzon Allah) ASHHADU AN LA’ILAHA ILLALLAH WA ANNAKA MUHAMMADUN RASULULLAH!!!.

 

ALLAH ya kara mana soyayyan Manzon Allah SAW Duniya Da Lahira. Amiin

Share

Back to top button