KISSA: Lokacin Da ‘Yan’uwan ANNABI YUSUF (A.S) Suka Zo Wajen Mahaifinsu ANNABI YA’AQUB (A.S) Da Rigar Shi (Yusufa).

‘KISSA (Mai Ban Tausayi)

 

A Lokacin Da ‘Yan’uwan ANNABI YUSUF (A.S) Suka Zo Wajen Mahaifinsu ANNABI YA’AQUB(A.S) Da Rigar Shi(Yusufa).

 

Sai Ya Ce:”Kai Wannan Kura Da Tausayi Take, Ta Yadda Ta Cinye YUSUF Amma Bata Kekketa Rigar Shi Ba”.

 

Sai Ya Fashe Da Kuka Mai Tsanani, Sai Mala’ika Jibrilu Ya Zo Wajen Shi(ANNABI YA’AQUB(A.S),

 

Ya Ce Masa:”Ka Yi HAKURI Mai Kyau(HAKURI Wanda Babu Raki Babu Kuma Kai ‘Kara a Cikin Shi)”.

 

Sai ANNABI YA’AQUB(A.S) Ya Runtse Idanuwansa, Kuma Ya ‘Boye Bakin Cikinsa a Cikin Ran Shi, Ya Ce:”HAKURI Mai Kyau”,

 

Shikenan Sai ALLAH Ya Sakawa ANNABI YA’AQUB(A.S) Barci.

 

Sai ALLAH(S.W.T) Ya Cewa Mala’ika Jibrilu:”Hakika YA’AQUB Ya Samu HAKURI Mai Kyau a Ran Shi”.

 

Sai Mala’ika Jibrilu Ya Sauko Zuwa Gare Shi a Surar YUSUF, Lokacin Da ANNABI YA’AQUB(A.S) Ya Gan Shi,

 

Sai Ya Fashe Da Kuka Ya Ce:”Ya Abin Da Rayuwa Take ‘Kauna!!!”.

 

Sai Mala’ika Jibrilu Ya Farkar Da Shi, Ya Ce Masa:”Ina HAKURI Mai Kyau ‘Din???”

 

Sai ANNABI YA’AQUB(A.S) Ya Damki ‘Kasa Ya Cika Bakin Shi Da Ita, Ya Ce: “ALLAH Na Tuba Zuwa Gare Ka”.

 

Sai Mala’iku Suka Fashe Da Kuka(Saboda Tsananin Tausayin ANNABI YA’AQUB(A.S).

 

Sai ALLAH Ya Cewa Mala’ika Jibrilu:

 

“Ka Shaidawa ANNABI YA’AQUB(A.S) Ya Zubar Da ‘Kasar Dake Cikin Bakinsa, Hakika Na Gafarta Masa, Kuma Na Yi Izini a Gare Shi Ya Iya Yin Kuka, SAI DAI KA DA YA KAI KUKAN SHI ZUWA GA WANI NA”.

 

Ya SALAAM😭😭

 

Ya ALLAH Ka ‘Kara Ba Mu Hakuri Da Juriya a Cikin Dukkan JarrabawarKA, Ko Da Bai Kai SABRUN JAMEEL Ba, Ameeeeen

Share

Back to top button