KISSA: Wani Daga Cikin Mutanen Kirki Ya Ziyarci MANZON (S.A.W) Sai Ya Tsaya ‘Kyam a Gaban ‘Kofa Yana Kallon Inda ANNABI (S.A.W) Yake.

‘KISSA:
…Wani Daga Cikin Mutanen Kirki Ya Ziyarci MANZOb(S.A.W) Sai Ya Tsaya ‘Kyam a Gaban ‘Kofa Yana Kallon Inda ANNABI(S.A.W) Yake, Ya ‘Daga Hannayensa Sama Yana Addu’a.
Sai Wani Mutum Daga Cikin Masu Tsaron Gurin(Askar) Ya Gan Shi, Ya Ce Da Shi:
“Ka Fuskanci Alqibla a Cikin Yin Addu’ar Ka.”
Sai Wannan Salihin Ya Ce Masa:
“Kai ‘Dana;
Ka’aba Ita Ce Alqiblar Yin Sallah, In Za’a Yi Sallah Ka’aba Ake Kalla.
Sama Kuma Ita Ce Qiblar Yin Addu’a, In Za’a Yi Addu’a Sama Ake Kalla.
Shi Kuma SHUGABAN HALITTA(S.A.W) Shi Ne Alqiblar Duk Abinda Kake Nema, Shi Ne Alqibla Ta, Shi Ne Alqiblarka Ranar Da Babu Ka’aba Babu Sama, Babu ‘Kasa, Ranar Qiyama Shi Kadai Ne Alqibla.”
Sallallahu Alaihi Wa Sallaam…
ALLAH Ka Tabbatar Da Mu a AlqiblarSA MUHAMMADUR-RASULULLAHI KANZIL MUGMIR (S.A.W) Amiin
Daga: Sidi Kabir Yola