KISSA: Wani Dattijo Ne Ya Tsufa Sosai Har Ta Kai Ba Ya Gane Mutane Idan Mutum Ya Shigo Dakinsa Sai Dai Ya Faɗi Sunansa Sannan Dattijon Ya Gane.

SHIN KA TAƁA JIN WANNAN?

 

Wani Dattijo Ne Ya Tsufa Sosai Har Ta Kai Ba Ya Gane Mutane.

 

Idan Mutum Ya Shigo Dakinsa Sai Dai Ya Faɗi Sunansa Sannan Dattijon Ya Gane. Sai Dai Akwai Wani Mutum Guda Ɗaya, Wanda Shi Yana Shigowa Dakin Nan Take Dattijon Zai Gane Shi, Ta Hanyar Kamshin Mutumin. Kullum Haka Yake Yi.

 

Rannan Sai Wannan Mutum Ya Shigo, Bayan Sun Gaisa Sai Dattijon Yace Masa “Wai Wane Me Yasa Bana Gane Kowa, Amma Kai Da Ka Shigo Sai Inji Kamshi, Kamshin Ya Fita Daban Shiyasa Kai Kadai Nake Ganewa”

 

Sai Wannan Mutumin Ya Cewa Tsohon “Lallai Ni Ban San Ya Akai Ba, Sai Dai Ni Na Kasance Mai Yawan Salatin Annabi Muhammadu RasulilLaHi SallallaHu AlaiHi Wa AliHi Wa Sallam ﷺ. Duk Tasbihina Da Zikirina Salatin Annabi Ne, Bani Da Wani Aiki Sai Shi. Rannan Na Kwanta Barci Sai Nayi Mafarki Da Manzon AllaH SallalLahu AlaiHi Wa AliHi Wa Sallam ﷺ Muna Zaune Mu Da Yawa Mun Zagaye Annabi. Sai Manzon AllaH Yai Mana Tambaya Yace “Wanene Ya Fi Yi Min Salati a Cikinku?” Duk Sai Mukayi Shiru. Ya Sake Tambayarmu, Har Sau Uku. Ba Wanda Ya Ba Shi Amsa.

 

Sai Ya Nuna Ni Yace “Kai Ne Ka Fi Yi Min Salati, Saboda Haka Taso Ka Zo Nan” Sai Na Mike Na Taso Na Zo Gaban Annabi. Sai Na Ga Ya Kamo Fuskata Ya Sumbaci Laɓɓana.

 

Daga Nan Na Farko, To Wannan Shine Yasa Kamshin Ya Gauraya Da Jini Da Numfashina, Sai Ya Rika Fitowa Ta Hancina Ya Zama Everytime Kamshi Nake Yi.” Wannan Shine Sirrin.

 

AllaH Ta’ala Ka Shaida Munyi Wa Annabi Salati SallallaHu AlaiHi Wa AliHi Wa Sallam ﷺ

Share

Back to top button