KISSA: Wata Rana Shehu Ngibrima Zulma Arif R.T.A Yakai Ziyararsa Zuwa Garin Jos Ya Sauka Masaukinsa Gidan Shehu Salihu Nakande.

JIYA BA YAU BA,

 

Watarana Shehu Ngibrima Zulma Arif R.T.A ziyararsa zuwa Garin-Jos ya sauka masaukinsa Gidan Shehu Salihu Nakande, A tare da shi akwai Shehu Musaddidu da Shehu Abubakar Bafillacen Faira, Allah Ya kara musu yarda,

 

Bayan dare ya fara yi anyi sallar Isha’i sai jama’a masu ziyara suka watse yarage saura su uku sai suka cewa Shehu muje makwancinka bayan sunje sai Shehu yana shiga dakin ya ga babban kafita da ake kira Number 1,

 

Shehu ya ce musu mainene wannan sai suka amsa masa cewa ai akansa zaka kwanta, buɗar bakin Shehu yace da su, Gibrima bazata zama Gibrima ba da take kwanciya akan katifa da duk kayan laushi da muke kwanciya akansu yanzu,

 

Shehu Ya ce nakai shekara 30 zuwa sama ban taɓa Kishingiɗa ba bare nayi gyangyaɗi ko Barci, lallai Shehu ya wuce misali fatan mu dai ALLAH Ya ba mu albarkacin masu albarka, Amin

 

Tushen Labari, Kalifan Shehu Bafillacen Faidah Sheik Ahmadu Tijjani Jos R.T.A

Share

Back to top button