KOGIN ILMI: Kusan Malaman Ku Tare Da Sheikh Malam Zubair Madigawa Kano.
Kogin Ilmi Sheikh Malam Zubair Madigawa Kano (Shahararren Malamin Islama)
An haifi Sheikh Zubairu Jibril Madigawa, a Ibadan a lokacin da mahaifinsa ke zaune a can, amma asalinsa mutumin Kano ne dake arewacin Najeriya.
Ya fara karatun boko a farkon shekara 1970, da karatun addini a gidansu kasancewarsa ɗan gidan malamai kuma akwai makaranta a gidan su.
Sai dai ya fara daukar karatu a gaban wani Mallam Hamisu, mutumin Sararin Karnuka a Kano dake zaune a birnin Ibadan jihar Oyo.
Daga baya mahaifinsa Malam Madingawa ya cire shi daga makarantar boko ya mayar da su wata makarantar Addinin wato islamiyya da Larabawan Masar suka buɗe, bayan sun samu ɗan lokaci sai mahaifinsu ya rasu a birnin Ibadan.
Bayan dawowarsu Kano, ya je makarantar firmare ta Gwamaja 1 sa’annan ya yi karatun sakandare a Kwalejin Rumfa a 1985. Haka kuma ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da zummar karantar ilimin sanin ma’adanan ƙasa (Geology).
A Zariya ya hadu da wasu malamai Nufawa a Unguwar Samaru, inda ya shiga bangaren Arabiya kamar Nahwu, Lugga, Sarfu da kuma makamantan su, wanda ya mayar da hanakalinsa kan karatun addini.
Daga karshe ya ajiye karatun digirin, ya mayar da hankalinsa kan neman ilimin addini baki daya. Bayan ya koma cikin garin Zariya, ya koma ɗaukar karatun zaure, na wasu shekaru.
Bayan komawarsa Kano, ya sake gano gidajen ƙarin wasu malamai masu yawa. Inda ya dauki karatu a gaban Sheikh Sani Kafinga.
Sheikh Sani Kafinga, ya tura shi wajen malamai masu yawa ciki har da Sheikh Sani na Ƙofar Doka da ke Zariya wanda hakan ya yi sanadiyar komawarsa can a karo na biyu.
Ya sake komawa Kano bayan wasu shekaru inda ya sake ɗaukar karatu a gaban Sheikh Malam Baban Kawu da Shehu Abul -Fatahi Maiduguri idan ya je Kano da Sheikh Yusuf Makwarari inda ya koyi tafsirin Alƙurani.
Ya kuma koma neman ilimin tsarkake ruhi na sufanci, a wajen Marigayi Sheikh Aliyu Harazimi, kafin daga bisani ya mayar da hankali kan harkokin hadisi.
Cikin bangarorin da suka wahalar da shi a karatu akwai littafin Shu’ara, sai littafin Fiƙihu na Askari saboda rashin sharhi.
Daga: BBC Hausa