‘Kokarin Kare Alfarmar Sahabbai (R.A) Mutum Ya Afkawa Mutuncin Ahlul-Baiti.

….Idan a ‘Kokarin Kare Alfarmar Sahabbai (R.A) Mutum Ya Afkawa Mutuncin Ahlul-Baiti Hakika Ya Zo Da Wata Cutar Wacce Tafi Zagin Sahabban Girma, DOMIN YA ZO DA NASIBANCI.

 

Haka Kuma In Garin Kishin Ahlul-Baiti(A.S) Mutum Ya Afkawa Mutuncin Sahabbai Ya Afkawa Hadari Don Ya Zo Da RAFIDHANCI.

 

Yana Da Kyau Duk Mai Sha Daga “MASHRABIN” Sufaye Ya Fahimci Matafiyarsu Akan Wannan Maudhu’in,

 

In Kuwa Ba Haka Ba, Ko Shi’awa Su Fizgi Fahimtarsa Ko Kuma Izalawa Su Farauce Ta.

 

Rudun Ya Taso Ne Daga “Ma’anar” Sahabi a Wurin Mabambantan Matafiyoyi.

 

Shi’awa Sun Takura Ma’anar Ta Yanda Wasu Wadanda Basa So Ba Zasu Samu Shiga Ba, Don Haka Ne “GULLATU” Daga Cikinsu Suke Fad’awa “RAFIDHANCI” Suna Ta6a Alfarmar Khalifofi Uku(3) Na Farko(R.A).

 

A ‘Dayan Hannun Kuma, Izalawa(Wahabiyawa) Sun Fad’ad’a Ma’anar Sahabi Ta Yanda Zasu Iya Saka Har Wadanda Ba Sahabban Ba, Kawai Don Suna Sonsu,

 

Ko Kuma Don Manufar Siyasa, Sukan Yi Hakan Duk Munin Aikin Wanda Suke Son, Kuma Duk Yanda Ke Akwai “NASSOSHI” Akan Rashin Ingancin Hali Da Imaninsa.

 

*** Maslaha Ita Ce; Matafiyar Ahlus-Sunna Wacce “JAMHOOR” Na Sufaye Suke Akai.

 

Amma Akan “QADHIYYAR” Imam Husaini(A.S) Da Yazeedu(L.A) Muna Kusa Da Shi’ah,

 

Kuma Kwata-Kwata Bama Tare Da Izala.

 

Hakan Ne Matafiyar “SADATU” Namu Shehu Tijani(R.A) Da Sheikh Ibrahim(R.A).

 

ALLAH Ka ‘Kara Dubun La’ana Ga Wanda Ya Kashe Imam Husaini (A.S), Ga Ibnu Ziyad Tare Da Yazeedu, Ameeen

Share

Back to top button