Kyawawan Dabiu Da Halayen Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari Hafizalullah.

DUKKANIN MUKHLISAI SUNYI ITTIFAKI A SHAIDA GARESHI AKAN:-

 

• Shi din fasihine mai baiwar ban mamaki a fannonin ilmin Addini, da fahimta faffada, wanda himma, hazaka da kokarinsa ya bambanta da dukkan tsara.

 

• Shi din ma’abocin aikine da ababen da yake fadi, ba za ka ganshi ya aikata sa6anin fadinshi ba.

 

• Shi din ma’abocin kyawawan halayene da dabi’u, da bai muzantawa ko aibatawa balle cutar da halitta ta kowacce fuska.

 

• Shi din ma’abocin son gusar da damuwoyin al’ummane, saboda jinkai da tausayi. Ya zamo silar bayar da magunguna da aka samu waraka daga dimbin cututtukan da suke addabar al’ummar Musulmi ta fuskar akida da fahimtar addininma baki daya.

 

• Shi din ma’abocin son hadin kan Musulmine da kullum yake fafuta akan hakan, kuma ya cimma nasarori akan hakan. Sannan ya kasance mai zaburar da matasa da son ganin sun ribaci lokacinsu mai tsada.

 

• Shi din ya kasance mai son girmama dukkaanin bayin ALLAH ne, balle kuma jagorori makusanta bai kasance mai tauye matsayin kowa ba.

 

• Shi din tafiyayyene a soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W), tafiya maras waige ciki.

 

• Shi din bai da buri face yaga Tijjanawa sun haura matsayi na kololuwa a dukkanin ababen da suka shafi harkokinsu na yau da kullum sun riska sun tserewa tsararsu.

 

•Shi din mai fadin abinda zai yardar da ALLAH ne cikin zantukansa, baya neman yardar da kowa, baya neman girma wajen halitta, sannan ba kasafai yake damuwa da cutar mahassada ba.

 

ALLAH YA KARA HASKAKA RAYUWARSA, YA KARA MASA LAFIYA DA SUTURA. AMIIIIN

 

Daga; Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button