LABARI MAI DADI; Wata Baiwar Allah Ta Karbi Kalmar Shahada A Garin Imo.

LABARI MAI DADI: Wata matar aure mai suna Chinonso ta koma Amina bayan ta musulunta a garin Owerri dake jihar Imo.

 

Matar auren ta bayyana cewa, sauyawar halayen da mijinta yayi zuwa kyawawa dabi’u bayan ya musulunta suka jawo hankalinta itama ta bi sahun shi ta karbi musulunci.

 

Legit ta ruwaito cewar Aisha Obi, matar auren da farko ta fusata bayan mijinta ya Musulunta, amma ganin canjin halayensa da kuma jin lamurran addini yasa ta bi sahu.

 

Allah ya tabbatar da ita cikin addinin Islama ya kara mata himma da kwarin gwaiwa. Amiin

Share

Back to top button