LABARI MAI SOSA ZUCIYA: Sheikh Lawan Maiguduma Gombe

LABARI MAI SOSA ZUCIYA(Yanda Abin Ya Kasance):
:
……..Bayan Idar Da ZIKIRIN JUMA’AH a Fadar Mai Martaba Sarkin Kano(Bayan Maghriba) Ranar Juma’ah, Ba Tare Da Wani ‘Bata Lokaci Ba, Kai Tsaye SHEIKH LAWAN MAI GUDUMA Ya Wuce Garin KIBIYA Cikin Jihar Kano Don Amsa Gayyatar Da Aka Yi Masa, Inda Ya Gabatar Da Wa’azi a Garin Bai Ta Shi Daga Majalisin Ba Sai Can Tsakiyar Dare(Dai Dai Misalin 01:00am) Na Dare, a Cikin Daren Suka Kamo Hanyar Komawa Gida(Gombe) Su Biyar Ne a Cikin Motar,
:
Sheikh Lawan Maiguduma Shi Ya Karbi Tuqin Motar, Sallar Asuba Ta Yi Musu a Garin Darazo, Bayan Kammala Sallar Ta Asuba Sheikh Yayi Doguwar Addu’ah Kafin Su Cigaba Da Tafiya, Bayan Sun ‘Dauki Hanya Sun Bar Darazo ‘Kadan, Sai Yake Gayawa ‘Daya Daga Cikin Khadiminsa Mai Suna Abdu(P.A ‘Dinsa) Yake Ce Masa; Giyoyin Motar Nan Wani Iri Nake Jinsu, Tunda Suka Bar Garin Darazon Yayi Maganar Nan Bai Sake Wata Magana Da Kowa Ba(Sai ZIKIRI Kawai Yake Ta Yi Kawai).
Sai Da Suka Je Check-Point Na Jami’an Tsaro Na Mashigar Garin Dukku Da Suka Tsaya Yayi Wa Jami’an Tsaro Bayanin Daga Inda Suke, Amma Kamar Hankalinsu Bai Kama Bayanin Ba, Sai Ya Fitar Musu Da I.D Card ‘Dinsa Ya Nuna Musu, Suka Bashi Hakuri Sannan Suka Nemi Yayi Musu Addu’ah, Yayi Musu Addu’ar Suka Wuce, Sheikh Ya Cigaba Da Zikirinsa, Bayan Sun Bar Garin Dukku Kadan Sai Hatsarin Da Ya Yi Sanadiyar Sheikh Da ‘Yarsa ‘Karama Ya Faru, inda Aka Karbi Ransa Harshensa ‘Danye Sharaf Harshensa Jiqe Da ZIKIRI.
Wani Abin Al’ajabi Ranar Juma’ah(Da Rana) Sheikh Ya ‘Kira Gidansa Ya Gaisa Da Iyalansa, Inda Daga Karshe Ya Ce a Baiwa Babban ‘Dansa Zai Yi Wata Magana Da Shi, Inda Yayi Wata Magana Mai Kama Da Ishara/Wasiyya Inda a Cikin Maganar Yake Cewa;
“Ko Rai Zai Yi Halinsa Akwai Harami Da Na Dawo Da Shi Daga Hajji (Saudiyya) Lokacin Da Na Yi Aikin Hajji Ku Rufe Ni Da Shi(a Madadin Likkafani) Sannan Ku Binne Ni a Cikin Zauren Nan Da Nake Baiwa Yara Karatu a Ciki”
Daga ‘Karshe Suka Yi Sallama Wannan Ita Ce Magana Ta ‘Karshe Da Yayi Da Gidansa.
Kuma Alhamdulillah! An Yi Kokarin Cika Dukkan Wadannan Wasiyoyin Da Sheikh Yayi.
YA SALAM!
Don Neman ‘Karin Bayani Za’a Iya Tuntubar Malam Abdu (Wanda Shi Ne P.A Na Sheikh Kuma Yana Tare Da Sheikh Lokacin Da Wannan Hatsarin Ya Faru) Ga Lambarsa Kamar Haka; 08080950018.
ALLAH Ka Ba Mu Kyakykyawan Karshe Mu Cika Da Kyau Da Imani,
ALLAH Ka Yarda Ka Amince Ka ‘Karbe Mu a Cikin Ambatonka Kamar Yanda Ka Yiwa Bawan Nan Naka. Ya Bar Gidansa Dominka, Ya Fita Ambatonka Dominka, An Gama Ambaton Kalmarka Da Shi Amma Ba Ka Amince Ya Koma Gida Ba.
ALLAH Ka Jaddada Rahamarka a Gare Sa, Ka Bamu Himma Irin Tasa a Cikinka Don Isar ‘Nasirul Haqqi Bil Haqqi’ AMEEEEN…