LARABGANA: Annabi SAW Yace: Ana Saukar Da Bala’o’I Guda Dubu Dari Uku Da Dubu Ashirin a Cikin Wannan Larabar ta Karshe a Watan Safar

LARABGANA (1445)

 

Allah SWT yana cewa:

 

“فَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحًا صَرْصَرًا فِي أَيَّامٍ نَّحِسَاتٍ لِّنُذِيقَهُمْ عَذَابَ الْخِزْيِ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۖ وَلَعَذَابُ الْآخِرَةِ أَخْزَىٰ ۖ وَهُمْ لَا يُنصَرُونَ

“Sai Muka aika, a kansu, da iska mai tsananin sauti da sanyi, a cikin kwanuka na shu´umci, domin Mu dandana musu azabar wulakanci, a cikin rayuwar duniya, kuma lalle azabar Lahira ita ce mafi wulakantarwa, kuma su ba za a taimake su ba.

 

Sayyidina Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam yace “Ayyamin Nihasatin” wato “kwanakin shu’umanci” Sune Ranakun Larabar Qarshe a watan safar wanda Ake kira LARABGANA

 

Annabi SAW yace: Ana Saukar Da Bala’o’I Guda Dubu Dari Uku Da Dubu Ashirin a cikin wannan larabar ta qarshe a watan safar.

 

Duk Bala’o’in Da Zasu Faru A Wannan Shekarar

To A Laraban Karshen Watan Safar Ake Saukar Dasu Zuwa Cikin Duniya, Kamar Yadda Duk Alkhairai Da Zasu Auku A Shekarar Ake Zubo Dasu A Daren Nisfu-Sha’aban.

 

Akwai Nafila da akeyi raka’a hudu (sallama ɗaya). bayan fatiha ana karanta “Inna A’aɗaina kal Kausar (17), Qulhuwallahu Ahad (5) falaqi (1) Nasi (1). Haka za ayi cikin kowani raka’a.

 

Bayan anyi sallama sai a karanta

“ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻏﺎﻟﺐ ﻋﻠﻰ ﺃﻣﺮﻩ ﻭﻟﻜﻦ ﺃﻛﺜﺮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻻ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ

WALLAHU GALIBUN ALA AMRIHI WALA KIN AKSARAN NASI LAA YA’ALAMUN (360)

 

Sannan a karanta JAUHARATUL KAMALI (3) sai a cika da faɗin:

ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺭﺑﻚ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺰﺓ ﻋﻤﺎ ﻳﺼﻔﻮﻥ ﻭسلاﻡ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺮﺳﻠﻴﻦ ﻭﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ

SUBHANA RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUN, WA SALAMUN ALAL MURSALINA, WALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMIN.

 

Qarin Bayani: In akayi sallar a jam,i yafi, amma babu laifi in mutum yayi shi kaɗai. Su kuma yara da tsofaffi da wanda bazai iya ba, sai a rubuta Wayannan ayoyin qafa daya a sha, gasu kamar haka:

1. سَلَامٌ عَلَيْكُمْ بِمَا صَبَرْتُمْ ۚ فَنِعْمَ عُقْبَى الدَّارِ

SALAMUN ALAIKUM BIMA SABARTUM, FA NI’IMA UQBAD DAAR.

 

2. سَلَـٰمٌ۬ قَوۡلاً۬ مِّن رَّبٍّ۬ رَّحِيمٍ۬

SALAMUN QAULAN MIN RABBIN RAHEEM.

 

3. سلام على نوح فى العالمين

SALAMUN ALA NUHIN FIL ALAMIN.

 

4. سلام على ابراهيم

SALAMUN ALA IBRAHIM

 

5. سلام على موسي وهرون

SALAMUN ALA MUSA WA HARUN

 

6. سلام على ءال ياسين

SALAMUN ALA ALI YASIN

 

7. سلام عليكم طبتم فادخلوها خالدين

SALAMUN ALAIKUM ĎIBTUM FAD-KHULUHAA KHALIDIN.

 

8. سلام هي حتى مطلع الفجر

SALAMUN HIYA HATTA MAĎLA’IL FAJR

 

Note: Gobe laraba 13 September 2023 itace ranar Larabgana, Allah ya kare mu, ya kiyaye mu, alfarmar Annabi SAW. Amiin

 

✍🏻Sidi Sadauki

Share

Back to top button