Lauyoyin suna neman kotu ta tilasta wa gwamnati biyan cikakken diyya ga duk wadanda harin ya shafa da kuma iyalansu.

Lauyoyin Arewa Za Su Maka Gwamnati A Kotu Kan Kisan Tudun Biri

 

Lauyoyin suna neman kotu ta tilasta wa gwamnati biyan cikakken diyya ga duk wadanda harin ya shafa da kuma iyalansu

 

Kungiyar Lauyoyi Masu Kishin Arewacin Najeriya na shirin maka gwamnatin kasar a kotu domin neman hakkin mutanen da jirgin soja ya jefa wa bom a yayin da suke gudanar da taron Mauludi a Jihar Kaduna.

 

Lauyoyin suna neman kotu ta tilasta Gwamnatin Tarayya biyan cikakken diyya ga duk wadanda harin ya shafa da kuma iyalansu.

 

Akalla mutum 120 ne suka rasa rayukansu a harin da jirgin ya kai kauyen Tudun Biri ranar Lahadi da dare, yawancinsu kananan yara da mata.

 

Da yake magana a madadin lauyoy9in, Barista Nafi’u Abubakar ya ce za su yi iya kokarinsu domin ganin duk wadanda da suka rayukansu da wadanda suka samu rauni da sauransu a harin, an biya su cikakken hakkinsu.

 

Da yake jawabi a taron manema labari da kungiyar ta gudanar a Kaduna ranar Asabar, kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi zuzzurfan bincike mai zaman kansa sannan ta dauki tsattsauran mataki a kan duk masu hannu a harin da aka kai wa mutnane da ba su ji ba, ba su gani ba.

 

“Dole ne kuma a dauki matakin hana sake faruwar haka, sannan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya wajibi ne ta yi gyaran fuska ga tsarin gudanar da aikinta da na ba da horo.

 

“A matsayinta na mai alhakin kare kasa da samar da tsaro, wajibi ne ta kasance mai matukar taka-tsantsan domin kiyaye rayukan fararen hula.

 

“Mu da iyalanmu muna jajanta wa al’ummar Tudun Biri, kuma muna bayansu 100% wajen ganin an yi adalci wajen ba su hakkinsu.

 

“Za mu yi aiki ba dare, ba rana domin ganin an biya su diyyar da ta dace da abin da ya auka musu.” in ji shi.

Share

Back to top button