Lokacin Da MADINAH Ta Cika Ta Tumbatsa An Yi Yawa, Unguwanni Sun ‘Karu Masallacin MANZON ALLAH (S.A.W) Yayi Nisa,
…DA ZASU YI MANA ADALCHI…
SAYYIDI BASHIR IBN MAULANA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI Yana Cewa;
“Lokacin Da MADINAH Ta Cika Ta Tumbatsa An Yi Yawa, Unguwanni Sun ‘Karu Masallacin MANZON ALLAH (S.A.W) Yayi Nisa,
Sai MA’AKI (S.A.W) Ya Nad’a Limamai a Unguwanni Daga Cikin Limaman Da Ya Nad’a Akwai Wanda Kullum Idan Ya Zo Zai Yi Sallah Bayan Ya Karanta FATIHA Da Sura Kamar Yanda Aka Saba Sai Ya ‘Dora; QULHUWALLAHU Akai,
Sai Mamunsa Suka Tambaye Shi Menene Yasa Kullum Idan Ka Yi Fatiha Da Sura Sai Ka ‘Dora Qulhuwa Akai,
Sai Ya Ce Musu Haka Kawai Na Ga Dama, Sai Suka Kai ‘Kararsa Wajen MANZON ALLAH (S.A.W),
MA’AIKI (S.A.W) Ya ‘Kira Shi Ya Ce Masa; Me Ye Yasa Kake ‘Dora Qulhuwallahu a Karatun Sallarka Bayan Fatiha Da Sura
Sai Ya Ce: Ya RASULULLAHI! Son Qulhuwallahu Nake Yi Shi Yasa Nake Haka,
Sai MA’AIKI (S.A.W) Ya Ce Masa; Jeka Idan Ka Ganka a Aljanna, To Son Qulhuwallahu Ne Ya Kai Ka,
~ Wannan Hadisi Imam Muslim Ne Ya Ruwaito Shi, a Babin Falalar Surar Qulhuwallahu,
To Jama’a Da Wad’ancan Mutanen Zasu Yi Mana Adalchi Akan Dukkan Abin Da Suke Tuhumarmu Akai Da Sai Su Tambaye Mu Su Ce Mana Kun Dame Mu Da Wa’ke-Wa’ke Na Yabon MANZON ALLAH (S.A.W),
Kun Cike Mana Gari Da Zanga-Zanga Wai Kuna Zagayen Maulidi Mu Abin Ya Dame Mu,
To Da Sai Su Yi Irin Yanda Mamun Can Suka Yi Ma Limaminsu Suka Yi ‘Kararsa Wajen MA’AIKI(S.A.W),
Mu Kuma, Idan MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Tambaye Mu Menene Yasa Muke Haka,
Sai Mu Ce; Ya RASULULLAHI! Wallahi SONKA Ne Yasa Muke Haka Wallahi,
Shike Nan Sai MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Ce:”Shike Nan Ku Je;
Almar’u Ma’a Man Ahabba,
‘Mutum Yana Tare Da MasoyinSA (S.A.W)”.
ALLAH Ya ‘Kara Mana ‘KAUNAR SAYYIDUL-WUJUDI(S.A.W), Ya ‘Kara Tsare Mana Imaninmu Ameeeeen