Manufar Sufaye Daban Da Kuma Manufar Wadanda Ba Sufaye Ba A Addinin Musulunci.

MMANUFAR SUFAYE, DABANCE DA MANUFAR WANCENANSU A:-

 

• Bautar ALLAH

• Soyayyar Janabai masu girma.

• Mu’amala da bayin ALLAH.

 

√ Manufa cikin Basufiyar Ibada ga ALLAH, ta bambanta da na Bawahabiya ko Ba Shi’iyiyar ibadar ALLAH, Sufaye na bautar ALLAH ne saboda shi ALLAH ya chanchanci ayi masa bautar ba tare da kowanne irin sababi ko dalili ba na maslahar kai.

 

Ya chanchanci aji tsoron jalalarsa ko da bai halicci wuta domin horo ba, sannan ya chanchanci ayi masa da’a ko da bai halacci Aljannah domin sakayya ba, su Sufaye basu cinikayyar lada da ALLAH cikin bautarsa, suna cinikayyar rayukansune cikin neman yardar ALLAH ومن الناس من يشري نفسه ابتغاء مرضات الله

 

√ Basufiyar Soyayyar Janabai masu tsarki, na da bamabanci da na Bawahabiya da kuma na Ba Shi’iyiyar Soyayya.

 

Cikin a abinda ya shafi soyayyar ANNABAWA baki dayansu, Sufaye basu tauye ko guda daga cikinsu, sabanin wancenansu Wahabiyya da suka kasance suna da tawaya a soyayyar fiyayyen halitta, haka zalika cikin abinda ya shafi Sahabbai Sufaye basu kasance a sashen “Nasibawa ba” wato masu fakewa da Kaunar Sahabbai suna muzanta Iyalan gidan MANZON ALLAH (S.A.W), haka nan basu kasance a sashen ‘Rafidawa ba’ masu fakewa da soyayyar Iyalan gidan MANZON ALLAH (S.A.W) suna muzanta Sahabban MANZON ALLAH (S.A.W).

 

Sufaye sun kasance masu girmama dukkanin Sahabbai, da iyalan gidan MANZON ALLAH (S.A.W) basu da ajin muzantawa ko kuma aibatawa a tsakaninsu. Haka zalika a soyayyar waliyyai ma sun kasance suna kaunar baki dayansu.

 

√ Mu’amalar Sufaye tsakaninsu da Sauran bayin ALLAH, mu’amalace mai cike da mutumtawa, girmamawa da kuma darajantawa, mu’amalace wacce ake ginata da zallar kyautata zato daga barin munanta zato, amfanarwa daga barin cutarwa, Maslaha daga barin fitina, yabo daga barin aibatawa, da kuma nemawa halitta dace da rahamar ALLAH daga barin la’ana da tsinuwa, Duk inda kaga Mu’amala sabanin haka, daga wani mai intisabi sa Sufanci, to ya tsintone daga wani gida a sabanin gidan Sufaye.

 

ALLAH YA DAUKAKA KIMA DA ALFARMAR SUFAYE, YA KASHEMU A TAFARKINSU, YA TASHEMU CIKINSU. Amiin

Share

Back to top button