MANZON ALLAH (S.A.W) Ba Irinmu Bane, Domin Da Kansa Yake Cewa.. ‘Ayyukum Ka Hai’atiy. Inji Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari

SHEIKH (Prof.) IBRAHIM AHMAD MAQARY (R) Yana Cewa:

 

“MANZON ALLAH (S.A.W) Ba Irinmu Bane, Domin Da Kansa Yake Cewa… ‘Ayyukum Ka Hai’atiy???

 

Ma’ana: Wanene Ke Da Structure Irin Tawa???”.

 

To Kuma Gaba ‘Daya Wadanda Suka Kafirce Ma Annabawansu Sun Kafirce Ne Saboda Sun ‘Dauka Kuma Sun Ce Annabinsu Mutum Ne Kamarsu…”,

 

‘Yan’uwa Mu Kula… A Kula… ANNABI Ba Irinmu Bane.. Halitta Ne Wanda a Hadisin Bukhari Aka Ruwaito Cewa:

 

Lokacin Da SAYYIDUNA ALI(R.A) Ya Hau Kan Kafadarsa Lokacin FATHU MAKKAH Sai Da Ya Ga Kamar Zai Iya ‘Dauko Taurarin Sama,

 

Ku Duba Tsawon Ka’aba Amma SAYYIDUNA ALI (R.A) Yana Hawa Kafadan ANNABI (S.A.W) Ya Ciro Wadannan Gumakan Kuma Ka’aba Kowa Ya San Tsawonta Dai… A Nutsu/Kula Dai”.

 

LA ILAHA ILLALLAH…

 

ALLAH YA ‘KARA TSARE MANA IMANINMU, YA ‘KARA MANA ‘KAUNAR SAYYIDUL-WUJUDI (S.A.W) AMEEEN

Share

Back to top button