Masu Ƙalubalantar Prof Maqari kashi uku ne, Tunda Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana gaskiya akan su.

Masu Ƙalubalantar Prof Maqari kashi uku ne:

 

1. Akwai waɗanda dama suna neman wata dama ne da zasu taɓa mutuncinsa saboda hassada da ta mamaye zuciyarsu, wasu saboda saɓanin Aqida wasu kuma saboda kawai salon faɗakawar sa da zantukan sa bai musu ba.

 

2. Akwai waɗanda kuma borin kunya da son kare ƙarya ne ya sa suke haka, kuma waɗannan sune ke cikin 80% din da prof ya ambata, mafi yawansu noƙewa zasu yi saboda sun san a wannan tsarin suke.

 

3. Sai kuma waɗanda sune suke cikin 20% percent din. Wannan suna ƙalubalantar prof ne saboda sun san ba haka suke ba, waɗanda a adalce basa ma buƙatar su yi wata magana saboda ai sun san ba haka suke ba, kuma sunsan akwai akasin hakan.

 

Idan ana maganar karatu, da kuma tabbacin akwai shi, to duk hassadar mutum da baƙin cikin sa ya san Prof. Ibrahim Maqari ya kai Malami, ba ma a karatun syllabus ba, har a gaban Maluman Zaure zasu tabbatar maka wannan ba Sheikh ɗin hayaniya ba ne.

 

A gefe guda dole prof zai iya kuskure kamar ko wani ɗan Adam, kuma za’a iya saɓawa dashi cikin mutuntatawa da girmamawa ko dan darajar kujerar da yake kai, balle kuma tsohon Malami ne da aƙalla yana da masaniya a inda ya koyar.

 

Na fahimci dama da yawa akwai burbuɗin hassada a zuciyarsu, kiris suke jira su ga wata ƙofa da zasu kutsa dan su taɓa mutuncin wasu, kuma Allah ya bayyana da yawan su, wasu mun gani wasu kuma an gane mana su.

 

Sabo Ibrahim Hassan

Share

Back to top button