Matasa Kutashi Tsaye Domin Neman Ilimin Addini Dana Zamani, Sheikh Barhama Daba.

Matasa Kutashi Tsaye Domin Neman Ilimin Addini Dana Zamani, Sheik Barhama Daba.

 

Daga Abdulazeez Ibrahim Hassan

 

An yi kira ga matasa da su nemi ilimin addini da na zamani domin su zama shugabanni nagari a nan gaba.

 

Shahararren malamin addinin musuluncin nan Sheikh Barhama Daba, shine yayi wannan kiran a yayin taron mauludin da aka gudanar a garin Kalmai dake karamar hukumar Billiri a nan jihar Gombe.

 

A cewar Sheikh Barhama Daba, ilimi shi ne kashin bayan samun duk wani ci gaba mai ma’ana, a don haka sai yabukaci matasa da su sadaukar da lokacinsu wajen neman ilimi domin samun kyakkyawar makoma.

 

Dangane da zaben 2023 mai zuwa kuwa, shehin malamin ya shawarci matasa da su kaurace wa shiga bangan siyasa, kuma su guji baiwa ‘yan siyasa marasa kishin kasa damar yin amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.

 

Sheikh Barhama ya kuma shawarci ’yan siyasa da su rika yin siyasa ba tare da gaba ba, kana su guji cin mutuncin juna a yayin gangamin siyasa domin a ci gaba da samun zaman lafiya kafin, yayin da kuma bayan zaben shekara ta 2023.

 

Allah yasa muyi zabe lafiya ya bamu shugabannin nagari. Amiin

Share

Back to top button