Matasan Tijjaniyya Kishin Su Na Kare Martaban Manzon Allah SAW Ne.

WALLAHI KISHINSU GA KARE MARTABAR MANZON ALLAH (S.A.W) BABU WASA KO SIYASA CIKINSA.

 

Mizanin aje komai a mahallinsa wani sa’in na shiga mawuyacin yanayi, ko ayayin da kai komon tunani ya haifar da chunkoson fahimtoci mabanbanta a cikin zuciya cikin waki’o masu sarkakiya dake bijirowa;

 

• Musamman duba ga cikekkiyar ladabi ga wani bangaren.

 

• Musamman duba ga wasu dake da kuntacecciyar tunani wanda suke fassara mutane sabanin manufofin zantukansu, da suka kasance basu iya aje ababe a mahallansu ba, sannan basu duba baya balle gaba, ayayin yanke hukunci akan zancen da ya bayyana garesu..face bakanta shafukansu da habaice-habaice munana.

 

To Amma idan muka duba girma irin na MANZON ALLAH (S.A.W) , sannan idan muka wai-waici irin muggan kalaman da aka kirkira aka jingina masa, sannan muka yantu daga nuna damuwa ga dukkan muguwar kalmar da za’a kirkira a jingina mana, sai muga ko da wanne irin sakamakone zai biyo baya idan muka bayyana gaskiyar abinda yake a waki’i, to lallai mun biya.

 

Duk wani mutum komabayan Manzanni, to bai da siffa ta Isma, mai yiwuwane ya aikata ababe na dai-dai masu tarin yawa, amma hakan baya nuna cewa “shi ba zai aikata kuskure ba, ko kuma ya fahimci wani abun akan kuskure ba”, wanda kuma mafi kyaun mu’amala da kowa shine “ku hadu a inda aka dai-daita, tare da yiwa juna uzuri cikin sabani”.

 

A cikin wadannan ranaku, wasu sun wanzu suna masu jifan wadannan gwarazan da kalmomi munana, mai yiwuwa ko dan saboda rashin fahimtar manufa da ma’anar zancen Maulana Prof. yadda ya kamata.

 

Har wasu idan aka ambaci batu na siyasa cikin sha’anin yanke hukuncin wannan mutum, sai su dinga suranta wadannan mazajen daga bangaren Tijjanawa suna musu wani kallon hadarin kaji, wanda a hakika hakan rashin adalcine, musamman idan mai yin hakan ya kasance ya bibiyi ababen da suka abku tsawon shekaru 3 zuwa 4, na irin tsagwaran gwagwarmayar da suka sha, domin kare kima da martabar MANZON ALLAH (S.A.W), da Sahabbansa da kuma Waliyyan ALLAH tare da kawar da dimbin sa6a lamba daga wannan Malamin.

 

Mai yiwuwa Mafarkin da nayi, tare da ganinsu a da’irar Raudar MANZON ALLAH (S.A.W) wani busharane da tabbaci agareni akan cewa “Lallai su din sam babu algus na kowanne irin son zuciya cikin fafutukarsu a kare martabar MANZON ALLAH (S.A.W). Domin wallahi naga mutum biyu daga cikinsu.

 

Saboda haka, duk wanda zaike kallonsu da wani kallo sabanin manufar da suke kai, to bai fahimci zancen Prof. ba, kuma bai musu adalci ba, domin da ace shi wancan Malami ya kawar da dagawa ya saurari gyararrakin da suke masa, to wallahi da babu masu farin ciki sama da su akan hakan, domin basu kasance suna kiransa ta hanyar kiyayyar zatinsa ba, sabanin dabi’unsa, face burinsu ya tuba ya gyara dan ya rabauta, saboda haka idan ma wasu ya zamo an samesu da siyasantar da batunnan, (Shima zatone) to lalllai su kam ina da tabbaci sam basu kan haka.

 

ALLAH YA SAKAWA MAULANA PROF. DA IJTIHADINSA, SU KUMA YA KARA DAUKAKA DARAJARSU, BISA JAJIRCEWARSU A KARE DARAJAR MANZON ALLAH (S.A.W). Amiiiin

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button