Matsayin Yazidu Dan Mu’awuya Agun Sheikh Ahmadu Tijjani (R.T.A)

Yazidu Agun Shehu Tijjani R.T.A!!

 

Zalunci Mafi Muni Shine Zaluncin da Yazidu yayi na kashe Jikokin Annabi S.A.W akan haƙƙin su.

 

Shine ya saka aka kashe Sayyadina Hassan, kuma ya saka aka kashe Sayyadina Hussain ƙaninsa, Wannan ba ƙaramin Zalunci bane ba.

 

Shiyasa mu Tijjanawa Muna tsinewa Yazidu Kamar Yadda Maulanmu Shehu Tijjani ya tsine mai a cikin Littafin

 

الإرشادات الربانية بالفتوحات الإلـٰهية

 

Sharhin da Shehu Yayi wa Hamziyya ta Imamul Busiri, Gun da yazo kan Ƙadiyyar da shi Busiri ke nuna ɓacin ransa da damuwa da Abubuwan da akayi na kisan gilla ga Jikokin Annabi S.A.W agun da yake fassara baitin:

 

من شهيدين ليس ينسيني الطفْٰ

فُ مصابيهما ولا كربلاء

 

Shehu Radiyallahu Anhu yace:

 

من شهيدين ليس ينسيني، أشار بهذا البيت إلى أنهما مقتولان معا

 

Wannan bitin yana nuni da cewa Dukkan su su Biyun Kashe su akayi.

 

أما الحسن فقتله يزيد بن معاوية، وذلك أنه بعث إلى زوجته إن سقته سما قاتلا أعطاها مائة ألف فسقته وعليه لعنة الله فهذا هو الشهيد أول.

 

Amma Sayyadina Hussain R.T.A Yazidu Ɗan Mu’awiyah ne ya kashe shi, ta hanyar turawa matar sa da Sanar da ita cewa, da zarar ta shayar dashi Sammu me kisa toh ze Bata dinare duba ɗari, ta kuma shayar dashi, Shehu Tijjani yace: Allah ya tsine masa. Wannan shine Shahidi na Farko.

 

والشهيد الثاني الحسين قتل بالطف من كربلاء وهو مكان مشهور من ناحية العراق، وهناك قتل في خمس مائة رضي الله عنه، فيهم ثلاثة وثمانون من بني هاشم ومنهم سبعة عشر من أولاد علي رضي الله عنه.

 

Yace: Shahidi na Biya Shine Sayyadina Hussaini wanda aka kashe a Ilɗuf a Karbala, guri ne Mashhuri a Nahiyar Iraƙ, acan aka kashe shi a cikin mutum Ɗari biyar, a cikinsu Akwai mutum 83 daga Banu Hashim Akwai kuma mutum 17 daga yaran Sayyadina Aliyu R.T.A.

 

Shehu a ƙarshen bayaninsa na wannan baitin ya ƙare tsinewa Yazidu da wanda ya saka ya kashe shi الشمر بن ذي الجوشن.

 

Kuma daman tsinannu ne da nassir Ƙur’ani Saboda sun cutar da Annabi S.A.W .

 

Allah kuwa ya faɗa cikin Cutar da Annabi a Alƙur’ani:

 

إن الذين يؤذون الله وروسوله لعنهم الله في الدنيا والآخرو وأعد لهم عذابا مهينا.

 

Wanda suka cutar da Allah da Annabinsa S.A.W Allah ya tsine musu a Duniya da lahira kuma ya tanadar musu Azabar Wulaƙanci.

 

Banjin Akwai cutar wa kamar a Kashewa Annabi S.A.W Jikoki Guda Biyu ya’yan ‘yarsa da yafi so tsokar sa.

 

A ƙarshe ina faɗa kamar yadda Busiri ya faɗa:

 

كل يوم وكل أرض لكربي

منهم كربلا وعاشوراء

 

Kowace Rana da Kowane Guri ga Bakin ciki na na wannan kisan Gillar, Karbala ne da Ranar Ashura.

 

Wannan ita ce Matsayar Maulanmu kan wannan Ƙadiyyar kuma muma akanta muke.

 

Amma Maganar Sahabbai da Abunda ya gudana tsakanin su wannan ba ruwan mu bazamu saka baki kamar yadda shima be saka baki ba zamu tsaya kan:

 

والإمساك أو الكف عما شجر بين الصحابة

 

Shima Yazidu ba Sahabi bane domin bega Annabi S.A.W ba kamar yadda Malaman Tarihi Suka tabbatar.

 

Allah ya jaddada tsinuwar sa ga Wanda sukayi wannan Kisan Gillar, ya kuma ƙara yarda ga shahidai Guda Biyu da aka kashe da Mahaifinsu da Mahaifiyar su da dukkan Sahabban Annabi S.A.W.

 

Daga: Shareef Ahmad Mukaddam

Share

Back to top button