Maulana Sheikh Dahiru Bauchi OFR RA Dan Gwagwarmaya Ne Tun Yana Yaro Har Yakai Tsufa Ba Dare Ba, Rana Cikin Aikin ALLAH

Maulana Sheikh rta tun yaranta gwagwarmaya take hana bacci har tsufa aikin Allah ba’a ritaya.

 

Haka aikin Allah take yadda ka dauketa haka take daukar ka riketa dakyau saita riƙeka da kyau harma ta bayyanaka ga al’umma ka riketa da wasa sai taama haka.

 

Darika hidima da himma da soyayya ita ke bayyana mutum daga ka rasa wayanna tofa sai dai ka zauna a gida ko kuma ka ringa bim gurare kana gaya musu kaine wane basuma sanka ba amma idan ka riƙi hidima kafin kaje guma an sanka domin buwar ta wuce ɓuya…

 

Wanda kaga baka san shiba ko baka ganinsa daidai hidimarsa kenan misali mai sauki daga hidimar Shehu Tijjani khudubul muktum sai da duniya ta sanshi misali daga hidimar Shehu Ibrahim Inyass rta saida duniya tasanshi misali daga hidimar Shehu Dahiru Usman Bauchi rta saboda duniya ta san shi amma duk wayannan an san sune akan lamarin Muslunci da Faida bawai akan wata lamarin duniya ba,

 

Sun kai matsayin da duk inda kagansu aikin Allah ake agun kodai da’awa ko karatu ko karantar wa ko yadda zaa sama wa al’ummar Annabi sallallahu alaihi wassallam mafi cikin lamuransu da yau da kullun domin saida suka zama wakila na ko wacce akida da addini su ko wani mutum na sune.. Basa yadda a chutar da kowa.

 

Tijjaniyya mazaje irin waɗannan take buƙata masu hidima da gaske ba masu birgima irin na wasummu a yau ba da sunan tijjaniyya.

 

Allah ya karawa Maulana Lisanul Faidah Sheikh Dahiru Bauchi OFR RA lafiya da daukaka. Amiin

Share

Back to top button