Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA Yana Fada A Cikin Tafsirin Sa Kamar Haka;

MAULANA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI YANA CEWA:-

 

“Idan Ka Dauki Dan Adam Ka Dunqule/Cure Shi Ka Saka Shi a Kwalba Ka Dauki Kwalbar Ka Buga Ta Da Garu/Bango Abu Uku Ne Zai Fita a Jikinsa Kamar Haka:-

 

*1. KASHI,

 

*2. FITSARI,

 

*3. JINI,

 

Wadannan Abubuwa Su Ne Dan Adam Yake Qunshe Da Su, To a Koda Yaushe Idan ALLAH(S.W.T) Yana Magana Da Dan Adam Yana Magana Ne Da Ruhinsa Ba Wannan Gangar Jiki Da Muke Gani Ba, Wannan Gangar Jikin Buhun Mutum Ne Ainihin Mutumin Yana Cikinsa, Sai ALLAH Ya Kawo Annabi MUHAMMADU(S.A.W) Sai Ya Zama Kamar Gasket Tsakaninmu Da Fadan ALLAH(S.W.T), Idan Kabi Manzon ALLAH(S.A.W) Kabi Bayin ALLAH Waliyai Magada ANNABAWA Sai Akama Ruhinka a Fisge Shi a Tsarkakeka Daga Datti a Kai Shi Can Wani Halara Inda Rayukan ANNABAWA Da Siddiqai, Yake a Ajiye a Wurin Ka Fita Daga Sahun Sauran Mutane Kenan.

 

To Idan Kana Buqatan Haka Sai Ka Hada Kai Da Bayin ALLAH Magada Manzon ALLAH(S.A.W) Su Baka Zikirori Safiya Da Maraice Don Ka Haura Ka Tafi Fadan ALLAH, ALLAH Ya Hadamu Da Bayin ALLAH Na Gari Masu Jagoranci Zuwa Fadan ALLAH (S.W.T)”

 

AMEEEN SHEIKH!

 

ALLAH YA QARAWA SHEHU LAFIYA DA JURIYA, YA KARE MANA SHI DAGA SHARRIN MAQIYA AMEEEN.

Share

Back to top button