Maulana Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari Hafizafullah.
KA GANE ARIFI NA HAKIKA CIKIN MU’AMALA DA DABI’A, RABU DA BATUN ‘YAN DA’AWAH.
• Shin da aka jarabceshi da wata jarrabawa ta yaya ya mu’amalci ALLAH, kururuwa da kokayya ya dinga yi, ko kuma godiya yayi…?
• Shin da aka daura masa wata amana ta bayin ALLAH, ya kyautata saukewa ko ha’inci yayi…?
• Shin zantukan da yake furtawa tsakanin gaskiya da karya wannene yafi yawa…?
• Shin ya ya yake wajen kamewa da gudu a neman shuhura, suna da nuna fifiko tsakaninsa da wasu, shin ya kasance mai boye kai ta hanyar Zuhudu da Tawadi’u ko mai son tallata kai..?
• Shin ko da abin fushi ya abku gareshi, tayaya ya iya sarrafa kansa daga aikata aikin da na sani daga baya..?
• Shin yaya ya kasance ta fuskar mutunta dukkanin bayin ALLAH ta fuskar barin tozartawa da muzantawa..?
• Shin ko da abin tsoro da firgici suka zo masa, yaya bambancinshi ya kasance da wancenansa wajen komawa zuwa ga ALLAH…?
• Shin yaya zuciyarsa ta tsira daga kowanne irin nau’i na hassada, hikidu, da kuma son cutar da halitta ta kowacce siffa. Balle abkuwar jefe-jefe da sauransu?
• Shin yaya tsantseninsa yake cikin matukar kiyaye dokokin ALLAH da koyi da sunnonin MANZON ALLAH (S.A.W)…?
• Shin ya ya kasance cikin son tallafawa bayin ALLAH da duk abinda yake dashi, shin ya kasance mai tsoron bayarwa saboda gudun rashi..?
• Shin da aka cutar dashi da nau’oin cutarwa, tsayawa yayi ramako ko kuma mayar da al’amari yayi zuwa ga ALLAH…?
• Shin da rashin jituwa ko sabani tsakanin ‘yan uwa ya wakana, ruwa yake yayyafawa ko kuma fetur ta hanyar muggan zantuka..?
• Shin da aka jarabceshi da Talauci ko kuma rashin Kudi, ga ALLAH ya koma yana nema agareshi ta hanyar sababi mai kyau, ko roko da barace-barace yakeyi wajen mutane ko wasu hikinkimu da dabaru?
DA SAURANSU.
Misalin duk wanda yake da’awar Ma’arifa, amma ya zamo dabi’unsa da halaye basu bambanta da na wadanda yake ma kallon Mahajubai ba, kamar Misalin Dan Sandane da aikinsa ya ginu akan kawar da cin hanci da karbar rashawa, amma sai ya zamto ya halatta hakan ga karan kansa.
KA GANE ARIFI NA CIKIN MU’AMALA, RABU DA BATUN DA’AWAH, DOMIN IDAN DA DA’AWAH NA DA TASIRI, TO FIR’AUNA SHI DA’AWAR ALLANTAKA MA YAYI FAQAT.
Daga: Muhammad Usman Gashua.