Maulana Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari Ya Halarci Taron Mauludin Manzon Allah SAW A Birnin Abuja.

Sheikh Imam Ibrahim Maqari Hafizafullah Ya Halarci Taron Mauludin Manzon Allah SAW.

 

Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari Zaria ya halarci babban taron Mauludin fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW wanda ya gudana a City Park Wuse II dake babban birnin tarayya Abuja.

 

Taron Mauludin wanda Sayyada Hallum Sheikh Sharif Umar Haidara ta shirya ya samu halartan manyan malamai da muqaddamai da sauran yan’uwa mata daga sassa daban daban na fadin najeriya.

 

Cikin manyan baki da suka samu halartan sun hada da Sheikh Ibrahim Maqari, Imam Mansur Kaduna, Sheikh Khalifa Ahmadu Bolari, Sayyadi Aminu Sheikh Dahiru Bauchi da yan’uwa masoya Manzon Allah SAW daga kasashen waje.

 

An gabatar da karatu akan tarihin Annabi SAW da halayen sa da kuma kyawawan dabi’un sa tare da liyafan cin abinci don murna da samuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ﷺ.

 

Allah ya kara mana soyayyan Annabi Muhammadu SAW, ya amfanar damu cikin kyawawan halayen sa duniya da lahira. Amiin

 

Babangida A. Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button