MAULANA SHEIKH, YA WALLAFA MAZAJE ZUWA MUSULUNCI, YA WALLAFA SU ZUWA KARBAR ADASHEN GATA.

SAMA DAI TA YI WA YARO NISA….!

 

Da wallafa litattafai shine alami na riskar makura a ilmin Addini da kuma hidimarsa, to da an gajiya da lissaafa adadin yawan litattafan da su Sayyadina Abubakar, Umar, Usman da Aliyu (Allah ya yarda da su) suka wallafa, amma da yawansu sun fi hidimtuwa zuwa ga wallafa mazaje zuwa Musulunci a maimakon wallafa litattafai, balma cikinsu akwai wadanda ko littafi guda basu wallafa ba.

 

Sannan da wallafa litattafai wadanda ke kunshe da dafi dake illata imanin bayin ALLAH, da haifar da ta’addanci, rena Janabin MANZON ALLAH (S.A..W) da jismantar da ALLAH, da Malaman Wahabiya suka wallafa, wallahi lakana wuridin Darika ga mutum guda ya fishi alkairi har a wajen ALLAH.

 

Litattafan da Mallam Gumi ya wallafa, babu guda da ya zamo karbabbe wajen Malaman Ilmi, domin litattafai ne da ke kunshe da illa da kuma barna wanda sharrinsu yafi alkairinsu yawa.

 

SHI KAM MAULANA SHEIKH, YA WALLAFA MAZAJE ZUWA MUSULUNCI, YA WALLAFA SU ZUWA KARBAR ADASHEN GATA, SANNAN KUMA YA WALLAFA SU ZUWA GA HADDAR AL-KUR’ANI.

 

ALLAH YA KARA LAFIYA DA KUSANCI.

 

Muhammad Usman Gashua.

Share

Back to top button